Tashin Hankali da Hotunan Tashin Hankali

Cikakken bayanin doka

CANZA SHIGA
Ra'ayin Doka
Mun fahimci cewa mutane suna da mabambantan halaye dangane da hoto mai sosa rai ko na tashin hankali. Domin kare masu amfani daga irin waɗannan abubuwa, muna cire abubuwan da suka fi tsanani na hoto mai ɗauke da bayani kuma muna ƙara laƙabin gargaɗi ga wasu nau'o'in abubuwa domin mutane su sani cewa yana iya zama na sirri kafin su latsa su duba. Muna taƙaita damar ƙananan masu amfani su ga abubuwan da ƙila ba su dace ba ko waɗanda ba su dace da shekarunsu ba. Ta yin haka, muna da burin samar da ƙwarewar mai amfani da ta dace, tare da ci gaba da samar da wuri don masu amfaninmu su bayyana ra'ayoyinsu.
Mun fahimci cewa masu amfani za su iya raba abu don haskakawa ko yin Allah wadai da ayyuka kamar take haƙƙin ɗan adam ko rikicin makamai. Dokokinmu suna la'aƙari da lokacin da aka raba abu a cikin wannan yanayin kuma suna ba da dama don tattaunawa da wayar da kan jama'a daidai da haka.
Game da tallace-tallacen da aka biya, muna samar da ƙarin kariya. Misali, abubuwan da aka ayyana a matsayin na sirri ba su cancanci a gudanar da su a cikin tallace-tallace ba. Muna kuma hana tallace-tallace da suka haɗa da hotuna da bidiyo masu tayar da hankali, masu ban tsoro, ko kuma masu takura tunani. Don ƙarin bayani, da fatan za a duba Tsarin Tallace-tallacenmu.
Kada a aike:
Hotunan mutane
Bidiyon mutane, rayayyu ko marasa rai, a wurare marasa alaƙa da lafiya, da ke nuna:
  • Yanke sassan jiki.
  • GaÉ“oÉ“in jiki a bayyane, kamar buÉ—aÉ—dun gaÉ“oÉ“in jiki, Æ™asusuwa, ko tsokar jikin mutane masu rai ko matattu;
  • Ƙonawa ko mutanen da suka Æ™one; ko
  • Yanke maÆ™ogoro.
Watsa-bidiyo kai tsaye na aiwatar da hukuncin kisa.
Kalaman Rashin Imani
Kalaman rashin imani su ne sharhi – kamar take ko jawaban – da ke nuna farin ciki ko jin daɗi daga wahalar da mutane ko dabbobi.
Muna cire
  • Kalaman rashin imani da aka yi ga hotuna (bidiyo da hotuna) da a wata hanya ke samun allon gargaÉ—i a Æ™arÆ™ashin wannan manufar, suna ba mutane shawara cewa abun da ke ciki zai iya zama na sirri; sai dai idan hotunan sun nuna ayyukan kare kai (misali, bidiyon wani wadda ke kare kansa daga ‘yan fashi da makami) ko kuma a muhallin asibiti (misali., hoton Æ™wararrun likitoci suna aiwatar da tiyata).
  • Bayyana kalaman rashin imani dangane da wahalar da dabbobi ke sha a hotuna, da hotunan da ke nuna dabbobi a raye daga baya kuma su mutu.
  • Bayarwa ko neman hotuna da aka goge ko kuma suka sami allon gargaÉ—i a Æ™arÆ™ashin wannan manufar, a lokacin da aka haÉ—a su da maganganun rashin imani.
Ga wannan bayanin, mukan haɗa da allon gargaɗi domin mutane su san cewa bayanin zai iya sanya damuwa mai hankali. Haka kuma mukan taƙaita damar ganin bayanin ga manya, ‘yan shekaru 18 zuwa sama.
Hotunan mutane
Bidiyoyin mutane, rayayyu ko marasa rai, a muhallin lafiya da ke nuna:
  • Yanke sassan jiki.
  • GaÉ“oÉ“in jiki a bayyane, kamar gaÉ“oÉ“in jiki a buÉ—e, Æ™asusuwa, ko tsokar jikin mutane masu rai ko matattu;
  • Ƙonawa ko mutanen da suka Æ™one, wanda ya haÉ—a a mahallin Æ™ona gawa; ko
  • Yanke maÆ™ogoro.
Hotunan mutane, rayayyu ko marasa rai, da suke nuna:
  • Yanke sassan jiki.
  • GaÉ“oÉ“in jiki a bayyane, kamar buÉ—aÉ—dun gaÉ“oÉ“in jiki, Æ™asusuwa, ko tsokar jikin mutane masu rai ko matattu;
  • Ƙonawa ko mutanen da suka Æ™one; ko
  • Yanke maÆ™ogoro.
Hotuna (bidiyoyi da hotuna) da ke nuna mutuwar tashin hankali ta wani mutum (da ya haɗa da lokacin mutuwarsa ko bayan mutuwar) ko mutumin da yake fuskantar wani sha’ani da ke barazana ga rayuwarsa (kamar mota ta buge shi, faɗowa daga waje mai nisa, ko yake fuskantar wasu munanan raunuka na zahiri).
Hotuna da ke nuna hukuncin kisa ga wani mutum (ban da watsa shirye-shirye kai tsaye).
Hotuna masu nuna cin zarafi (misali, ayyukan tashin hankali ko barazanar kisa ga waɗanda aka kame da ƙarfi) da aka yi wa mutum ko gungun mutane.
Hotunan da ke nuna abubuwa na waje waɗanda ba na likitanci ba (misali., wuƙaƙe, ƙusoshi, ko wasu abubuwan ƙarfe) suna huda fatar mutum.
Hotunan da ke nuna karyewar haƙora, zubar jini daga haƙora, cire haƙora a inda ake ganin jini; ko kuma saka wani abu a cikin haƙora ko dasashi.
Hoton dake nuna ‘yan tayi da jarirai a wajen mahaifa waɗanda suka mutu, sai dai idan akwai wani mutum a hoton.
Hoton dabbobi
Duk wani hoto na dabbobi, masu rai ko matattu, – da ke nuna an yanyanke musu gaɓoɓi, ana iya ganin kayan cikinsu, an ƙone su ko sun ƙone, ko kuma ana dafa su da ransu.
Hoton dabbobi da ke nuna lokacin da suke mutuwa.
Hoton mutane suna aikata mugunta a kan dabbobi masu rai (misali, shura da ƙafa, nutsarwa a ruwa, ko fisge gashin tsuntsu).
Domin waÉ—annan abubuwan masu zuwa, mun iyakance damar duba su ga masu amfani waÉ—anda shekarunsu suka kai 18 zuwa sama:
Hotunan mutane
Hotuna da ke nuna gawarwakin mutane da ke tsirara ko wani ɓangaren jikinsu, ko da kuwa babu wata alama da ke nuna mutuwar tashin hankali.
Hoton dake nuna ‘yan tayi da jarirai a waje da mahaifa waɗanda suka mutu, yayin da akwai wani mutum a hoton.
Hotuna da ke nuna allurai suna huda fatar mutum a waje da mahallin allurar riga kafi, acupuncture ko allurar majina, ko gyaran jiki (misali, yin zane) ba a yarda dasu ba.
Hoto da ke nuna mutanen da suka ji rauni a yanayin rashin lafiya lokacin da suka bayyana suna cikin ciwo ko wahala, suna da rauni, ko tare da bututun magani a fuskokinsu da/ko hannayensu.
Hotuna da suke nuna wasu abubuwan da mutum ke fitarwa a jiki (misali, kashi, fitsari, amai, dattin kunne, majina, abubuwan da ake fitarwa daga fata, ko jini)
Hotunan da ke nuna motoci suna ƙonewa ko fashewa, ko kuma hotunan lokacin da motoci masu gudu suka yi karo da wasu abubuwa inda motar ta fice daga hanyarta da / ko ɓangaren direba ko fasinja sun sami mummunar lalacewa.
Hoton dabbobi
Hoto da ke nuna dabbobi, masu rai ko matattu, inda ake iya ganin jini.
Hotuna masu nuna dabbobi a lokacin haihuwa (misali, akwai jini ko ciki a bayyane).
Hoto da ke nuna dabbobi, masu rai ko matattu, inda ake ganin ƙwari suna fitowa daga jikinsu (misali, tsutsotsi).
Hoto da ke nuna dabbobin da suka ji rauni suna shan wahala.
Hotunan Almara
Hoto da ke nuna mutanen almara a cikin waÉ—annan yanayi masu zuwa:
  • Yanke sassan jiki;
  • Abubuwan da ke cikin jiki da ake iya gani, kamar gaÉ“oÉ“in jiki da aka tona, Æ™asusuwa, ko nama;
  • Mutanen da ke Æ™onewa ko waÉ—anda suka Æ™one;
  • Yanke maÆ™ogoro; ko
  • Mutuwa ta hanyar rikici ko sha'anoni masu barazana ga rai.
Hotunan mutanen almara waÉ—anda suka yi kama sosai da na gaske (wato, hotunan da suke kama ko suke yi kusa da hoto ko bidiyo na ainihin mutum), a cikin mahallai masu zuwa:
  • Abubuwan waje waÉ—anda ba na magani ba (misali, wuÆ™aÆ™e, Æ™usoshi, ko wasu kayan Æ™arfe) suna huda fata;
  • Ƙazantar mutum ko ruwan jiki (misali, bahaya, fitsari, amai, dattin kunne, majina, ko wani abu da aka cire daga fata), ban da jini;
  • jarirai ko Æ´an tayi matattu a wajen mahaifa;
Hotuna masu nuna dabbobi na dabara, amma masu kama da na gaske, a cikin yanayin da aka bayyana a ƙasa:
  • Yanke sassan jiki;
  • Abubuwan da ke cikin jiki da ake iya gani, kamar gaÉ“oÉ“in jiki da aka tona, Æ™asusuwa, ko nama;
  • Dabbobi masu Æ™onewa ko waÉ—anda suka Æ™one;
  • Dafa dabbobi da rai;
  • Akwai jini;
  • Dabbobi da ke a raye suna zama matattu;
  • Mutane suna aikata mugunta (misali, shura da Æ™afa, nutsarwa, ko fisge gashin tsuntsu) ga dabbobi masu rai;
  • Dabbobin da suka ji rauni suna shan wahala
  • Dabbobi da Æ™wari na fitowa daga cikinsu (misali, tsutsotsi).
Don waɗannan Tsarin Rayuwar Al'umma, muna buƙatar ƙarin bayani da/ko a muhallin da za a tilasta:
Ba ma ba da damar:
Hotuna ko sautuka na mummunar mutuwar mutum lokacin da aka tabbatar da mutuwar ta hanyar bayanan hukumar tsaro, ko takardar shaidar mutuwa, ko rahoton Abokin HulÉ—a Amintacce, ko kuma rahoton kafafen yaÉ—a labarai, kuma wani daga cikin iyalin mamacin ya nemi a cire su.
Bidiyon mutanen da suka ƙone ko suke kan ƙonewa a muhallin ƙona kai a matsayin wata hanya ta yin zanga-zanga.
Za mu iya yarda da:
Hotuna na mummunar mutuwar mutum ko na lamari mai barazana ga rai inda ba shi ne ainihin abin da ake nunawa ba
Ƙwarewar mai amfani da kaya
Duba wasu misalai na yadda ɗabbaƙa doka take ga mutanen da suke kan Facebook, kamar: yadda zai kasance wajen kai rahoton abin da kake ganin bai kamata ya kasance a Facebook ba, a faɗa maka cewa ka karya dokar Tsarin Rayuwar Al'ummarmu da kuma ganin allon gargaɗi a kan wani bayani.
Lura: A kullum muna ƙara ingantawa, saboda haka ta yiwu abin da ka gani a nan tsoho ne idan aka kwatanta shi da abin da muke amfani da shi a yanzu.
KWAREWAR MAI AMFANI
Kai rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Sadarwa bayan rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Kwarewar sauke abu
KWAREWAR MAI AMFANI
Allunan gargaÉ—i
Bayanai
Duba sabon bayani game da Rahoton Tilasta Bin Tsarin Rayuwar Al'umma
Ɗabbaƙa doka
Muna da manufofi iri É—aya a duk faÉ—in duniya, ga duk waÉ—anda ke kan Facebook.
Ma’aikata da ke sake dubawa
Ƙungiyarmu ta duniya da ke ɗauke da masu bita sama da 15,000 suna aiki kowace rana don kare lafiyar mutane a Facebook.
Aiki tare da masu ruwa da tsaki
Ƙwararru daga waje, malamai, ƙungoyoyin da ba na gwamnati ba da masu tsara dokoki suna taimakawa wajen samar da Tsarin Al'ummar Facebook.
Sami taimako a kan tashin hankali da hotunan tashin hankali
Sami bayani a kan abin da za ka iya yi idan ka ga wani abu a Facebook da ya saɓa wa Tsarin Al'ummarmu.
Ziyarci Cibiyar Taimakonmu