Tarkacen saƙo

Cikakken bayanin doka

CANZA SHIGA
Ra'ayin Doka
Ba mu yarda da abubuwan da aka tsara don yaudara, ɓatarwa, ko mamaye masu amfani da kaya don ƙara yawan masu kallo ba bisa ƙa'ida ba. Wannan abun na rage damar da mutane ke da ita ta shiga tattaunawar gaskiya a dandalinmu kuma zai iya yin barazana ga tsaro, zaman lafiya, da amfani da ayyukanmu. Haka kuma muna neman hana dabarun cin zarafi, kamar yaɗa mahaɗan ɓatarwa don jawo hankalin masu amfani da ba su sani ba ta hanyar ɓatar da aiki ko lamba, ko yin sojan gona ga amintaccen hurumi.
Sifam ta intanet sana'a ce mai riba. Dole ne manufofinmu da gano abubuwa su kasance masu ci gaba da canzawa tare da kunno kai da dabarun sifam. A wurin ɗaukar mataki don yaƙar sifam, muna neman a daidaita ƙaruwar kuɗin mai masu samarwa da masu rarraba shi a kan dandalinmu, tare da kare ayyukan al'ummarmu na gaskiya wadanda ke da maƙukar amfani.
Ba ma ba da damar:
  • Wallafawa, yaɗawa, yin mu’amala da bayani ko ka ƙirƙirar asusu, Kungiyoyi, Shafuka, Sha’anoni ko kadarori, da hannu ko mai sarrafa kansa, akai-akai.
    • Za mu iya saka iyaka a kan asusan da ke aiki a matakan ƙasa a lokacin da wasu alamu na Sifam (alal misali, tura saƙonnin da ake maimaitawa) ko alamun rashin inganci suke nan.
  • Yunƙurin ko yin nasarar sayarwa, saye, ko musayar kadarorin dandali, irinsu asusu, ƙungiyoyi, shafuka, da dai sauransu.
  • Yunƙurin ko yi nasarar sayarwa, saya, ko musanya matsayi na musamman a shafin, kamar rawar da mai gudanarwa ko mai kula da shafin ke takawa, ko izinin aikewa da saƙonni a wurare na musamman.
  • Yunƙurin ko yin nasarar sayarwa, saye, ko musanya abu domin wani abu mai darajar kuɗi, sai dai Nau’in Talla Mai Ɗauke da Bayanai da aka bayyana a fili, kamar yadda aka bayyana shi a Dokarmu ta Nau'in Talla Mai Ɗauke da Bayanai.
  • Yunƙurin ko yin nasarar sayarwa, saya, ko musanya don samun shiga, kamar so, raba bayanai, dubawa, bi, dannawa, amfani da alamun hash na musamman, da dai sauransu. Wannan ya haɗa da:
    • Bayar da kyaututtuka (wato, ba wa wasu damar cin gajiyar kyauta) ta kuɗi ko abubuwan da suka yi daidai da kuɗi don samun shiga. (misali, "Duk wanda ya so shafina zai shiga don samun damar cin gajiyar $500")
    • Tayin bayar da wani abu mai darajar kuɗi a matsayi musanyawa don kasancewa. (misali, "Idan ka so shafina, zan ba ka iPhone!")
  • Buƙatar ko kuwa iƙirarin cewa ana buƙatar masu amfani da su kasance da abu (kamar su, so, tare da rabawa) kafin su sami damar dubawa ko yin hulɗa da abun da aka yi alkawarin ba su.
  • Rarraba abun da ke yaudararwa ko URL mai ɓatar da mutane, hurumi ko manhajoji har da:
    • Rufewa: : Ɓoye abu shine duk wani yunƙuri na kauce wa manufofin abubuwan cikin mu ta hanyar gabatar da abubuwan ciki daban-daban na waje, kamar URL ko aikace-aikace, ga tsarin mutuncin mu ba kamar yadda aka nuna wa masu amfani ba.
    • Kafafe Masu Ɓatarwa: Abun da yake ɗauke da kafa da ta yi alkawarin wani nau’in abun guda ɗaya amma ta ba da wani abu daban. Wannan na iya haɗawa da abun a manhajar da aka yi alƙawari ko softwaya.
    • Wasu halaye na yaudara: Yanar gizon da ke buƙatar aiki (misali captcha, kallon talla, danna nan) don a duba abubuwan da ake tsammani na shafin saukewa ne kuma sunan hurumin URL ɗin ya canza bayan an kammala aikin da ake buƙata, ko kuma a sake tura masu amfani zuwa wani hurumin daban ba tare da wani aiki na mai amfani ba.
    • So/rabawa-kula da nau'in masu sauraro: Bukatar masu amfani su shiga (ta hanyar so, rabawa, bi, ko duk wata hanyar shiga ta jama'a) don samun damar shiga takamaiman abubuwan ciki na musamman.
    • Yadda yaudarar dandali ke aiki - Kwaikwayon sigogi ko aikin ayyukan mu, kamar kwaikwayon tara kuɗi, zaɓen ra'ayi, maɓallan kunnawa, ko maɓallin So inda wannan aikin babu shi ko kuma ba ya aiki kamar yadda ake tsammani, don sa mai amfani ya bi wata kafa.
    • Yanayin aiki na shafin da za a isa na yaudara: Shafukan yanar gizo da suke da yanayin amfani da ke yaudararwa, wanda ke haifar da haɗarin samar da cunkoso (kamar pop-ups/unders, clickjacking, da dai sauransu). Wannan ya haɗa da dabaru kamar tarko, inda abubuwa marasa amfani ke bayyana idan mutum ya yi ƙoƙarin barin shafin.
    • Kwaikwayon shafin sauka ko yanki - Shafin sauka na wajen dandali, URL, ko gidan yanar gizo na waje ko yanki wanda ke yin kamar alama ce ko sabis mai suna ta hanyar amfani da suna, yanki ko abubuwan ciki waɗanda ke da kurakurai, rubutu mara kyau ko wasu hanyoyi don kwaikwayon shahararrun gidajen yanar gizo, yankuna ko alamomi ta amfani da shafin sauka mai kama da wani shafin da aka amince da shi.
    • Sauran yaudarar na amfani da URLs ko kafafen da suka yi kama sosai da waɗanda ke sama.
  • Ba tare da la'akari da abin da ke sama ba, ba mu haramta:
    • Tallatawar da ba biyan kuɗi ga wani ɓangare can daban ba ne ya haifar da ita
    • Tura alhakin ayyukan mai gudanarwa ko mai kula don wani shafi ko ƙungiya ga wani mai amfani la’aƙari da sha’awar da suke da ita a shafin ko ƙungiyar, maimakon musanyar ƙimar kuɗi.
    • Aikewa ko raba Nau'in Talla Mai ɗauke da Bayanai Masu Tambari.
Ƙwarewar mai amfani da kaya
Duba wasu misalai na yadda ɗabbaƙa doka take ga mutanen da suke kan Facebook, kamar: yadda zai kasance wajen kai rahoton abin da kake ganin bai kamata ya kasance a Facebook ba, a faɗa maka cewa ka karya dokar Tsarin Rayuwar Al'ummarmu da kuma ganin allon gargaɗi a kan wani bayani.
Lura: A kullum muna ƙara ingantawa, saboda haka ta yiwu abin da ka gani a nan tsoho ne idan aka kwatanta shi da abin da muke amfani da shi a yanzu.
KWAREWAR MAI AMFANI
Kai rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Sadarwa bayan rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Kwarewar sauke abu
KWAREWAR MAI AMFANI
Allunan gargaɗi
Bayanai
Duba sabon bayani game da Rahoton Tilasta Bin Tsarin Rayuwar Al'umma
Ɗabbaƙa doka
Muna da manufofi iri ɗaya a duk faɗin duniya, ga duk waɗanda ke kan Facebook.
Ma’aikata da ke sake dubawa
Ƙungiyarmu ta duniya da ke ɗauke da masu bita sama da 15,000 suna aiki kowace rana don kare lafiyar mutane a Facebook.
Aiki tare da masu ruwa da tsaki
Ƙwararru daga waje, malamai, ƙungoyoyin da ba na gwamnati ba da masu tsara dokoki suna taimakawa wajen samar da Tsarin Al'ummar Facebook.
Sami taimako a kan sifam
Sami bayani a kan abin da za ka iya yi idan ka ga wani abu a Facebook da ya saɓa wa Tsarin Al'ummarmu.
Ziyarci Cibiyar Taimakonmu