Karya Dokar Sirri
Cikakken bayanin doka
CANZA SHIGA
Yau
2 Okt, 2024
26 Yun, 2024
29 Yun, 2023
23 Fab, 2023
29 Sat, 2022
24 Fab, 2022
24 Nuw, 2021
30 Sat, 2021
18 Nuw, 2020
30 Nuw, 2018
29 Yun, 2018
Ra'ayin Doka
Ayyukanmu suna nufin kare sirrin da kuma bayanan sirri na masu amfani da kayanmu. Muna aiki tuƙuru don kare bayananka da kuma bayanan sirrinka kuma ba ma ba da dama ga mutane su yi aike da wasu nau'ikan bayanai na ƙashin kai ko kuma na sirri game da kansu ko na wasu. Haka kuma mukan samar wa mutane hanyoyi don kawo rahoton hotuna da mutane suka yarda cewa sun saɓa wa ‘yancin sirrinsu.
Mukan cire bayanin da ke yaɗa, yin tayi, ko yake neman bayanan da ake gane mutum ko wasu bayanai na sirri da za su iya cutarwa ta zahiri ko ta kuɗi, da ya haɗa da bayanan kuɗi, wurin zama, da na lafiya, gami da bayanan sirri da aka samu daga haramtattun hanyoyi. Kuma mun yarda cewa bayanan sirri za su iya zama na bainar jama’a ta hanyar kawo labarai, bayanan kotu, jawaban ‘yan jarida, ko wasu hanyoyin. Yayin da haka ta faru, mu ma za mu iya bari a wallafa bayanin.
Muna da ƙarin taƙaicewa ga ƙunshiyar da aka biya Ko da yake muna amincewa da tallace-tallacen da ke ba da kyakkyawar ƙwarewa ga mai amfani ta hanyar mai da hankali kan cikakkun bayanai game da kayayyaki ko sabis, muna cire tallace-tallacen da ke amfani da wahalhalun mutum, waɗanda suka yi kama da yin mummunar fassara ko ba da bayanai waɗanɗa da daidai game da su, ko kuma nuna masaniya dangane da muhimman bayanan sirri. Don ƙarin bayani game da dokokin sirrinmu a kan abun da ake biya, duba Tsarin Tallanmu a kan Karya Dokar Kare Sirri da Siffanta Kai.
Ba ma ba da damar:
Abubuwan da ke yaɗawa ko tambayar bayanan sirri, ko a cikin ayyukanmu ko ta hanyar kafar waje, kamar haka:
Bayanan gano mutum (PII)
- Abun da ke raba Bayanan Gano Mutum (bayani da ke gano ɗaiɗaikun mutune musamman) mai sakawa ko wasu. Wannan ya haɗa da:
- Lambobin shaidar ɗan ƙasa kamar lambobin tsaro na zamantakewa (SSN), lambobin fasfo ko lambobin shaidar biyan haraji na mutum (ITIN).
- Katunan Shaida na Gwanmati na jami’an kula da doka, sojoji, ko jami’an tsaro.
- Takardu ko takardun shaida na hukuma mai bayanan rajistar jama'a kamar aure, haihuwa, mutuwa, canjin suna ko takardun shaidar jinsi.
- Takardun jami’an shege da fice da na matsayin aikin kamar su green card, izinin aiki ko visa
- Abun da ke neman Bayanan Gano wasu Mutanen
Bayananka na Tuntuɓa na ƙashin kai
- Abun ke raba bayanan tuntuɓar wasu, sai dai idan mutumin da abin ya shafa ya bayyana shi a bainar jama'a ko kuma idan aka raba domin dalilan neman ƙarfafa taimakon jama'a, taimakawa wajen neman mutanen da suka ɓace, dabbobi, ko masu kayan da suka ɓace, ko kuma tuntuɓar wani kasuwanci ko samar da wani aiki (sai dai idan an tabbatar da cewa an raba bayanan sirri ba tare da amincewar mutumin ba).
Bayanan wurin zama
- Abubuwan da ke raba cikakken adireshin gidan wasu na sirri, wanda ya haɗa da sunan gini ko lambar gano mutum a kan taswirar da ke nuna adireshin (ko da kuwa lambar gano mutum ba sa kan kafar dandali), sai dai a cikin waɗannan mahallan:
- Idan aka raba domin dalilai na ƙarfafa ayyukan taimako, taimakawa wajen gano mutanen da suka ɓata, dabbobi, ko waɗanda suka mallaki wasu abubuwa da suka ɓata, ko tuntuɓar wani kasuwanci ko masu samar da wani aiki
- idan wurin zaman gidan ne na gwamnati ko ofishin jakadanci da aka ba wani babban jami'in gwamnati.
- Raba abu wanda ya dangance wani yanki na adiresoshin wurin zaman wasu (sai dai idan gidan ya kasance gida ne na gwamnati ko ofishin jakadancin da aka ba wani babban jami'in gwamnati):
- A lokacin da aka raba a muhallin shirya zanga-zanga ko sa ido kan mazaunin sannan kuma an gano wurin zaman ta hanyar ɗaya daga cikin wadannan:
- Hanya
- Birni ko unguwa (kawai don biranen da ke da mazauna ƙasa da 50,000)
- Lambar Aika Saƙo
- Maɓalan GPS ko maɓallai a kan taswira da ke gano ɗaya daga cikin waɗannan (ko da maɓallan suna kan ko wajen mahaɗin dandali)
- Hoton da yake nuna ɓangaren waje na gidajen jama’a idan dukkan waɗannan sharuɗɗan suna aiki:
- Wurin zaman gidan iyali ɗaya ne, ko ana gane lambar layin gidan/ginin a cikin hoton/taken.
- Ana gano wurin zama da ɗaya daga cikin waɗannan:
- Hanya
- Birni ko unguwa (kawai don biranen da ke da mazauna ƙasa da 50,000)
- Lambar Aika Saƙo
- Maɓalan GPS ko maɓallai a kan taswira da ke gano ɗaya daga cikin waɗannan (ko da maɓallan suna kan ko wajen mahaɗin dandali)
- Bayanin yana gane mazauni.
- Ko dai wannan mazaunin ya ƙi amincewa da bayyana mazaunin suna keɓe, ko kuma akwai yanayi na shirya zanga-zanga kan mazaunin gidan
- Ba a raba hoton gidan saboda gidan shi ne jigon labarin (sai dai idan an raba shi a muhallin shirya zanga-zangar adawa da mazaunin gidan)
- Abun da ke neman bayanan sirri game da wurin da wani ke zaune (sai dai idan gidan ya kasance gida ne na gwamnati ko ofishin jakadancin da aka ba wani babban jami'in gwamnati)
- Abu da ke neman wurin na gidaje masu kariya ko fallasa bayanai game da gidaje masu kariya ta hanyar raba wani daga cikin waɗannan (sai dai lokacin da gidajen da ke da kariya ke ƙarfafa bayanai game da abubuwansu)
- Haƙiƙanin adireshi (Lura: An amince da “Akwatin Aika Wasiƙa” kawai)
- Hotunan mafakar
- Bayyana gari/unguwa da ke da gida mai kariya
- Bayanai da ke fallasa bayanan shaida mazauna gidan da ke da kariya
Bayanin kiwon lafiya
- Rarraba bayanai ko neman bayanan kiwon lafiya, na ƙwaƙwalwa, nazarin halittu, ko bayanan gado na wasu (ciki har da idan an nuna ko rabawa ta hanyar sauti ko bidiyo),idan an bayyana a fili cewa bayanan na zuwa daga bayanan da aka tattara na lafiya ko wasu takardu na hukuma.
Bayanan kuɗi
- Abubuwan da ake yaɗawa ko neman bayanin sirrin harkar kuɗi game da mai aike ko wasu mutanen, wanda aka bayyana a matsayin bayanai game da harkokin kuɗin ɗaiɗaikun mutane ciki har da:
- Ajiyayyun bayanan kuɗi ko jawabai da ba na bainar jama’a ba.
- Lambobin asusun banki tare da lambobin sirri na tsaro ko pin.
- Bayanan hanyar biyan kuɗi ta na’ura tare da bayanan shiga ciki, lambobin sirri na tsaro ko pin.
- Bayanin katin amsar da biyan kuɗi tare da ranakun wa’adin aiki ko lambobin sirri na tsaro ko pins.
- Abubuwan da ake rabawa ko neman bayanan kuɗi na sirri wanda ba na kasuwancin jama’a ba ko ƙungiya, waɗanda aka bayyana a matsayin bayanai game da kuɗin kasuwanci ko ƙungiya, sai dai lokacin da ƙungiyar ta raba shi da kanta (gami da rabawa ta gaba tare da mahallin asali) ko rabawa ta hanyar buƙatun rahotannin jama'a (misali kamar yadda musayar hannayen jari ko hukumomin ƙayyadewa suka buƙata), ciki har da:
- Ajiyayyun bayanan kuɗi ko jawabai da ba na bainar jama’a ba
- Lambobin asusun banki da ke tafe da lambobin sirri na tsaro ko pin.
- Bayanan hanyar biyan kuɗi ta na’ura tare da bayanan shiga ciki, lambobin tsaro ko pin.
Bayanan da aka samu daga wuraren da aka yi kutse
- Bayanin da mai aikawa ya yi iƙirarin ko ya tabbatar an samo shi daga wurin da aka yi wa kutse, ba tare da la’aƙari da ko dai wanda abin ya shafa wani fitaccen mutum ne ko kuma wani keɓeɓɓen mutum.
Wannan bayanin shi ma za a iya cire shi:
- Hoto ko bidiyon mutane da aka kawo rahotonsa inda mutumin da aka nuna a cikin hoton yake:
- Yaro ɗan ƙasa da shekaru 13, kuma yaro ne ko mahaifi ko mai riƙo na doka ya kawo rahoton bayanin.
- Yaro ɗan tsakanin shekaru 13 da 18 kuma yaro ne ya kawo rahoton bayanin.
- Babban mutum, a inda babba ne ya kawo rahoton bayanin daga wajen ƙasar Amurka inda kuma dokar da ke aiki za ta iya samar da damar cirewa.
- Duk wani mutum da yake da naƙasa kuma ba zai iya kawo rahoton bayanin da kansa ba.
Don waɗannan Tsarin Rayuwar Al'umma, muna buƙatar ƙarin bayani da/ko a muhallin da za a tilasta:
- Nuna Mutane & Wuraren Lafiya, wanda aka ayyana a matsayin abun da ke nuna mutum a asibiti ko wani wurin kula da lafiya ko wani mutum mai zaman kansa ko ƙaramin yaro da ke shiga ko fita daga asibiti ko wurin kula da lafiya, kuma an ba da rahoton shi daga:
- Mutumin da ke cikin hoton
- Wakilin mutumin da ke cikin hoton
- Asibiti ko wurin kula da lafiyar da ke da alhakin kula da mutumin da ke cikin hoton, ko
- Asibiti ko wurin kula da lafiyar da ya ɗauki mutumin da ke cikin hoton aiki
- Wurin samun kaya da ake zaton bayyana makamantan bayanai da ba na bayyawa jama’a ba na wani zaɓe da aka yaɗa a matsayin wani ɓangarre na tasirin aikin gwamnatin wata ƙasa.
- Mun cire rahoto kan irn wannan fitan labari da kafar watsa labarai ƙarƙashin ikon kulawar jiha daga ƙasar da ke bayab wannan fitar labari
Ƙwarewar mai amfani da kaya
Duba wasu misalai na yadda ɗabbaƙa doka take ga mutanen da suke kan Facebook, kamar: yadda zai kasance wajen kai rahoton abin da kake ganin bai kamata ya kasance a Facebook ba, a faɗa maka cewa ka karya dokar Tsarin Rayuwar Al'ummarmu da kuma ganin allon gargaɗi a kan wani bayani.
Lura: A kullum muna ƙara ingantawa, saboda haka ta yiwu abin da ka gani a nan tsoho ne idan aka kwatanta shi da abin da muke amfani da shi a yanzu.
KWAREWAR MAI AMFANI
Kai rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Sadarwa bayan rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Kwarewar sauke abu
KWAREWAR MAI AMFANI
Allunan gargaɗi
Ɗabbaƙa doka
Muna da manufofi iri ɗaya a duk faɗin duniya, ga duk waɗanda ke kan Facebook.
Ma’aikata da ke sake dubawa
Ƙungiyarmu ta duniya da ke ɗauke da masu bita sama da 15,000 suna aiki kowace rana don kare lafiyar mutane a Facebook.
Aiki tare da masu ruwa da tsaki
Ƙwararru daga waje, malamai, ƙungoyoyin da ba na gwamnati ba da masu tsara dokoki suna taimakawa wajen samar da Tsarin Al'ummar Facebook.
Sami taimako a kan karya dokar sirri
Sami bayani a kan abin da za ka iya yi idan ka ga wani abu a Facebook da ya saɓa wa Tsarin Al'ummarmu.
Ziyarci Cibiyar Taimakonmu