Bayanan Ƙarya
Cikakken bayanin doka
CANZA SHIGA
Yau
8 Afrilu, 2025
14 Mar, 2025
8 Jan, 2025
19 Yul, 2024
10 Yul, 2024
11 Yun, 2024
21 May, 2024
7 Fab, 2024
6 Dis, 2023
30 Sat, 2023
15 Yul, 2023
Ra'ayin Doka
Bayanan ƙarya ya sha bamban da sauran angarorin kalaman da ake gabatarwa a cikin al’ummarmu saboda babu wata hanya da za a fito da cikakken jerin abubuwan da aka haramta. Da hotunan zubar da jini ko ɗabiʼar ƙiyayya, alal misali, dokokinmu sun fayyace abubuwan da muka haramta, kuma har mutanen da ba su yarda da waɗannan dokokin ba za su iya bin su. haka kuma, da bayanan ƙarya, ba za mu iya samar da wancan layin ba. Duniya tana canzawa a kodayaushe, sannan abin da ya kasance gaskiya zai iya zama ƙarya a cikin minti ɗaya. Haka kuma mutane suna da bambancin matsayin labarai a game da lamuran duniya, kuma za su iya yarda da wani abin gaskiya ne alhali kuwa ƙarya ne. Dokar da ta haramta “labaran ƙarya” ba za ta samar da sanarwa mai amfani ba ga mutanen da suke amfani da ayyukanmu kuma ba za a tilasta masu ba, saboda ba mu da damar shiga bayanai.
A maimakon haka, dokokinmu sukan fito da bambance-bambancen rukunonin bayanan ƙarya da kuma ƙoƙarin samar da kyakkyawan hanyar yadda za mu ɗauki wancan kalami a lokacin da muka gan shi. Ga kowane rukuni, tsarinmu ya shafi yunƙurinmu na daidaita dokokin bayananmu, kiyayewa, mutuntawa, ingantawa, da kuma keɓancewa.
Mun cire bayanan ƙarya daga inda za su iya kawo wani haɗari kai tsaye da zai haifar da mummunan yanayi a fili. Kuma muna cire bayanan da za su iya kawo shigowar tasirin ayyukan siyasa da kuma yawan yaudara daga gurɓatattun kafar yaɗa labarai. Wajen gano abin da ya haifar da bayanan ƙarya a waɗannan ɓangarori, mun haɗa guiwa da kwarraru masu zaman kansu waɗanda suke da ilimi da kuma kwarewa a kan bibiyar gaskiyar bayanai da kuma in ko za su iya kawo mummunan yanayi. Waɗannan sun haɗa da, ga misali, haɗa guiwa da kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam tare da bayyanarsu a ƙasa don gano gaskiyar ji-ta-ji-ta a gameda rikicin siyasa.
Ga dukkan sauran labarai mara gaskiya, muna duba ne a kan raguwar yaɗuwa ko ƙirƙirar wani yanayi da zai kawo yanayin tattaunawa mai kyau. Mun sani cewa mutane sukan yi amfani da bayanan ƙarya a hanyoyin rashin cutarwa, kamar wajen samar da wani batu (“Wannan ƙungiya tana da tarihi mafi muni!”) ko wajen cin mutunci ko gugar zana (“Mijina ya zama gwarzon shekara.”) Kuma za su iya nuna kwarewarsu ta hanyar labaran da za suka ƙunshi rashin daidaito. A wasu wurare, mutane sukan tura ra’ayoyin kansu waɗanda wasu suke masu kallon ƙarya ko raba labarin da suka yi imanin gaskiya ne amma wasu na yi masa kallon bai inganta ba ko mai ɓatarwa.
Gane yadda irin waɗannan kalamai suka zama ruwan dare, muna mai da hankali wajen ba masu amfani bayanai masu taimako idan akwai abubuwan da ke iya ɓatarwa ko ruɗarwa. A irin wannan ƙoƙarin ne, a wajen ƙasar Amurka muna haɗa guiwa da ƙungiyoyin masu bincika-gaskiya na daban a ɓangarorin duniya da dama don sake duba da ƙimanta daidaito na bayanai da suka yawaita a dandalin mu (duba anan da nan don hanyarmu a Amurka). Tun daga Amurka, shirin Tsokacin Al'umma yana ba mutane damar ƙara ƙarin bayani zuwa Facebook, Instagram da kuma aiken Threads waɗanda za su iya zama masu ɓatarwa ko rikitarwa (duba a nan). Kuma muna samar da kayayyakin aiki don bunƙasa kafar yaɗa labarai da kuma koyo da koyarwa ta fasahar zamani ta yadda mutane za su san irin abin da za su karanta, gasgatawa, da kuma yaɗa kansu. Muna buƙatar mutane su bayyana, ta amfani da kayan aikin bayyanawa na AI, duk lokacin da suka wallafa bayani marar talla tare da bidiyo mai hoton gaske ko sautin murya na gaske wanda aka ƙirƙira ko aka jirkita da na’ura, sannan za mu iya ɗaukar mataki idan ba su yi hakan ba. Haka kuma za mu iya ƙara wata alama ga wani bayanin da aka ƙirƙira ko aka jirkita na’ura da ke ƙirƙirar abubuwa masu haɗari ko ɓatar da mutane game da abin da ya shafi jama’a.
Daga ƙarshe, mun haramta bayani da kuma hallaya a wuraren da ake samun yawan yaɗuwar labaran ƙarya. Ga misali, haramta Tsarin Rayuwar Al'ummarmu asusun ƙarya, zamba, da ɗabi'u na gari da aka haɗe.
A yadda cikin intanet da wajenta yake canzawa da kuma jujjuyawa, za mu ci gaba da sassaya waɗannan manufofi. Shafuka wanda suke maimata yaɗa bayanan ƙarya da aka jero a ƙasar nan, had da samun an cire bayansu yadda wannan manufar me ya fada, za su iya gani sun sami raguwar rarrabawa, ƙayyadewa a kan damarsu ta tallata, ko a cire su daga dandamalanmu. Za a iya samun ƙarin bayani a kan abin da zai faru idan Facebook ta cire bayanaia nan.
Jagorori
Bayanan ƙarya da muka cire:
Mun cire waɗannan nau'ukan bayanan ƙaryar:
I. Cutarwa a Zahiri ko Rikici
Mun cire bayanan ƙarya ko ji ta ji ta da ba a tantance ba wanda ƙwararru abokin hulɗa suka haƙiƙance akwai yuwuwar bayar da gudunmuwa kai tsaye ga haɗarin yawaitar rikici ko cutarwa a zahiri ga jama’a. Mun bayyana bayanan ƙarya a matsayin bayanai masu iƙirarin cewa akwai yiwuwar su zamo ƙarya daga wani can daban. Mun bayyana ji ta ji ta a matsayin iƙirarin da ƙwararru abokan hulɗa suka tabbatar da tushensa abu ne mai wuya ko wanda bai yiwuwa wajen bibiya, ga wanda ba a samu tushensa a hukumance ba.
Mun san cewa wasu lokuta bayanan ƙarya za su iya bayyana a farko, a bayani na musamman, bayar da gudunmawa ga haɗarin cutarwa ba ta intanet ba, da ya haɗa da bibiyar rikici da zai iya haddasa haɗarin mutuwa, mummunan rauni, ko wata cutarwa a zahiri. Muna aiki da hanyar sadarwa ta duniya ta ƙungoyin da ba na gwamnati ba (NGOs), ba don ƙungiyoyin cin riba ba, ƙungiyoyin jin ƙan al’umma, da ƙungiyoyin ƙasashen duniya da ke da ƙwarewa a waɗannan ƙananan halaye.
A cikin ƙasashen da ke fuskantar matsanancin haɗarin tashin hankali na al'umma, muna aiki tare da abokan hulɗa na gida don fahimtar wace da'awar ƙarya ce za ta iya ba da gudummawa kai tsaye ga haɗarin cutarwa a zahiri. Sannan muna aiki don ganowa da cire abubuwan da ke yin waɗannan da'awar a kan dandalinmu. Misali, a cikin tuntuɓar ƙwararru na gida, muna iya cire kafofin watsa labarai da ba su da tushe da ke ƙaryar da'awar nuna ayyukan tashin hankali, waɗanda abin ya shafa ko masu aikata tashin hankali, makamai, ko kayan aikin soja.
II. Bayanan Ƙarya Masu Cutar da Lafiya
Mukan tuntunɓi hukumar lafiya da ke jagoranci wajen tantance bayanan ƙarya da suka shafi lafiya waɗanda akwai yiwuwar samar da yawan haɗari kai tsaye ga lafiyar al’umma da kuma tsaro. Bayanan ƙarya masu cutar da lafiya waɗanda muka cire sun haɗa da:
- Bayanan ƙarya a game da riga-kafi. Mun cire bayanan ƙarya musamman a game da riga-kafi lokacin da hukumomin kula da lafiyar al’umma suka gano cewa bayanan ƙarya ne kuma tamkar bayar da gudunmuwa ne kai tsaye wajen ƙaruwar ƙin amincewa da rigafin. Sun haɗa da:
- Alluran riga-kafi suna haddasa cutar da ke taɓa ƙwaƙwalwa (Mis: “Ƙaruwar alluran rigakafi shi ne dalilalin da ya sa yara da yawa suke da cutar da ke taɓa ƙwaƙwalwa a yanzu.”)
- Alluran rigakafi suna haddasa Cuta Mai Saurin Kashe Jarirai (Mis: “Shin ba ka san alluran rigakafi suna kawo SIDS ba?”
- Alluran rigakafi suna haifar da cuta a jikin wanda da aka yi nufin su kare, ko su yi wa mutumin da ke karɓar riga-kafin sanadiyar da zai iya kamuwa da cutar (Mis: “Haƙiƙa yin allurar rigakafi yana sanyawa ka kamu da cutar tun da akwai yankin cutar a ciki. Yi hattara!”)
- Alluran rigakafi ko mahaɗansu suna iya kisa, illa, masu guba, cutarwa, ko haɗari (Mis: “Tabbas, za ka iya yin alluran rigakafi, idan ba ka gudun sanya guba a jikinka ba.”)
- Garkuwar jiki ta ɗabi’a ta fi amince a kan kariyar da allurar rigakafi ke bayarwa (Mis: “Kamuwa da cutar ya fi kariya a kan yin allurar rigakafin.”)
- Yana da haɗari a yi alluran rigakafi da yawa a ɗan gajeren lokaci, koda kuwa likitoci ne suka bayar da shawarar wannan lokacin (Mis: “Ka da ka yi allurar rigakafi sama da ɗaya a lokaci guda, hakan yana da haɗari - ba ruwa na da abin da likitanka ya faɗa maka!”)
- Alluran rigakafi ba su da tasiri wajen hana cutar da ake tunanin su kare. Duk da haka, ga alluran rigakafin COVID-19, cutar mura, da zazzaɓin cizon sauro, ba ma cire iƙirarin cewa waɗannan alluran rigakafi ba su da tasiri wajen kare wani mutum daga kamuwa da ƙwayoyin cututtukan. (Mis: Cire – “Allurar rigakafin cutar shan inna ba ta yin komai wajen hana ka kamuwa da cutar”; Cire – “Haƙiƙa alluran rigakafin ba sa yin komai wajen hana ka kamuwa da cututtuka”; Ƙyale – “Allurar rigakafin ba ta kare ka daga kamuwa da COVID-19, hakan ne ya sa za ka ci gaba da ba da tazara da sanya takunkumin fuska lokacin da ka ke tare da wasu.”)
- Kamuwa da cutar ƙyanda ba zai iya haddasa mutuwa ba (yana buƙatar ƙarin bayani da/ko yanayi)_(Mis: “Ka da ka damu game da ko ka kana da cutar ƙyanda, ba za ta zama mai haɗari ba.”)
- Vitamin C yana da tasiri kamar alluran rigakafi wajen hana kamuwa da cututtukan da aka samarwa da alluran rigakafi.
- Bayanan ƙarya game da lokacin kula da lafiyar al’umma cikin gaggawa. Muna cire bayanan ƙarya lokacin al’amuran gaggawa kan lafiyar jama’a yayin da hukumomin kula da lafiyar jama’a suka zartar da cewa bayanin na ƙarya ne kuma kai tsaye zai iya haddasa samun cutarwa a zahiri, da ya haɗa da ta hanyar haddasa ɗaiɗaikun mutane su sami ko yaɗa wata mummunar cuta ko ƙin amincewa da rigakafin mai alaƙa da wannan. Muna gane kula da lafiyar al’umma cikin gaggawa tare da haɗin guiwa da ƙanana da manyan hukumomin duniya.
- Bunƙasa ko yaɗa wasu hanyoyin magance haɗarurrukan da suka shafi lafiya. Waɗannan sun haɗa da karɓar magani a inda aka tabbatar, a fannin lafiya, kamar bayar da gudunmuwa kai tsaye wajen haɗarin samun babban rauni ko ma mutuwa, sai kuma kulawar da ba a yi amfani da dokar lafiya ba (mis: bilich, maganin kashe ƙwayoyin cuta, hoda, sabulu).
III. Shigowar Ƙidaya ko Zaɓe
A ƙokarin bunƙasa ingancin zaɓe da ƙidaya, muna cire bayanan ƙarya da za su iya bayar da gudunmuwa kai tsaye wajen afkuwar haɗari ga ƙoƙarin da mutane ke yi wajen shiga waɗannan shirye-shiryen. Wannan ya ƙunshi abubuwa masu zuwa:
- Bayanan ƙarya a game da kwanan wata, wurare, lokaci, da hanyoyin kaɗa ƙuri’a, rijistar mai zaɓe, ko shiga ƙidaya.
- Bayanan ƙarya game da wanda zai iya jefa ƙuri’a, cancantar yin zaɓe, ko za a ƙirga ƙuri’a, kuma waɗanne bayanai ko kayayyaki ya zama dole a samar kafin a yi zaɓe.
- Bayanan Ƙarya a game da shin ko ɗan takara yana yi ko a’a.
- Bayanan ƙarya game da wanda zai iya shiga ƙidaya da kuma yadda dole ne sai an tanadi bayanai ko kayan aiki don a halarta.
- Bayanan ƙarya game da shigowar gwamnati cikin harkar ƙidaya, da suka haɗa da, inda aka halasta, cewa za a tura bayanan mutum na ƙidaya ga hukumar gwamnati (da ba ta ƙidaya ba).
- Iƙirarin ƙarya ko wanda ba a tantance ba wanda Amurka Jami’an shige-da-fice da na Hana Fasa-ƙwauri (ICE) suna na a wurin zaɓe.
- Iƙirarin bayyana ƙarya cewa mutane za su kamu da COVID-19 (ko wata cutar da ake ɗauka) idan sun halarci wajen zaɓe.
- Iƙiraran ƙarya game da halin da ake ciki a wani wurin zaɓe na Amurka wanda zai sa a kasa yin zaɓe, kamar yadda hukumar zaɓe ta tantance.
Muna da ƙarin dokokin da ke da nufin daƙile faruwar tarzoma, ƙaruwar aikata laifuffuka, da kiraye-kiraye a kan harkar kula da zaɓe, wanda suke a cikin wasu sassa na Tsarin Mu’amalar Al'umma.
Domin bayanin da ke zuwa, mun sanya wata alama mai lurarwa:
Kafafen Sadarwa Da Aka Sarrafa
Za a iya gyara kafar yaɗa labarai ta hanyoyi da dama. A wurare da dama, a hankali waɗannan canje-canje, kamar ƙara bayanin da aka yanke ko gajarta a dalilin waƙa ko kiɗa. A wasu lamuran, ba a gane jirkitawar inda zai iya ruɗar mutum.
- Abubuwan da Aka Ƙirƙira na Dijital ko aka Jirkita dake iya Ɓatarwa. Amma abubuwan da ba su saɓa wa Tsarin Rayuwar Al'umma ba, za mu sanya alama mai lurarwa a fuskar ƙunshiyar – ko a ƙi amincewa da ƙunshiyar da aka miƙa a matsayin talla – yayin da abun ya kasance hoto ko bidiyo na zahiri, ko sautin murya na gaskiya, da aka ƙirƙira ta dijital ko aka jirkita kuma aka ƙirƙira musamman da abubuwa masu haɗari don yaudara jama’a game da abubuwa masu muhimmanci ga jama’a.
Ƙwarewar mai amfani da kaya
Duba wasu misalai na yadda ɗabbaƙa doka take ga mutanen da suke kan Facebook, kamar: yadda zai kasance wajen kai rahoton abin da kake ganin bai kamata ya kasance a Facebook ba, a faɗa maka cewa ka karya dokar Tsarin Rayuwar Al'ummarmu da kuma ganin allon gargaɗi a kan wani bayani.
Lura: A kullum muna ƙara ingantawa, saboda haka ta yiwu abin da ka gani a nan tsoho ne idan aka kwatanta shi da abin da muke amfani da shi a yanzu.
KWAREWAR MAI AMFANI
Kai rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Sadarwa bayan rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Kwarewar sauke abu
KWAREWAR MAI AMFANI
Allunan gargaɗi
Ɗabbaƙa doka
Muna da manufofi iri ɗaya a duk faɗin duniya, ga duk waɗanda ke kan Facebook.
Ma’aikata da ke sake dubawa
Ƙungiyarmu ta duniya da ke ɗauke da masu bita sama da 15,000 suna aiki kowace rana don kare lafiyar mutane a Facebook.
Aiki tare da masu ruwa da tsaki
Ƙwararru daga waje, malamai, ƙungoyoyin da ba na gwamnati ba da masu tsara dokoki suna taimakawa wajen samar da Tsarin Al'ummar Facebook.
Nemi taimako dangane da bayanan ƙarya
Sami bayani a kan abin da za ka iya yi idan ka ga wani abu a Facebook da ya saɓa wa Tsarin Al'ummarmu.
Ziyarci Cibiyar Taimakonmu