Amfani da Haƙƙin Mallaka da Lasisin Meta

Cikakken bayanin doka

CANZA SHIGA
Ra'ayin Doka
Meta tana ware manyan albarkatu don haɓakawa, kariya, da amfani da kadarorin fasaha ta yadda ya dace. Wannan doka tana taimakawa wajen tabbatar da cewa ba a yi amfani da kadarorin fasahar Meta ba, ta yanda ba bisa ƙa'ida ba, ba tare da rubutaccen izininmu na farko ba, ko ta hanyar da ba ta dace da Cibiyar Samar da Kayan Aikinmu ba.
Kar a aika abubuwan da ke:
  • Amfani da samfuri:
    • Amfani da haƙƙoƙin mallaka ko alamun kasuwancin Meta ba tare da izini a rubuce daga Meta ba ko kuma ta hanyar da Cibiyar Samar da Kayan Aikin Meta ta haramta.
    • Yana wakiltar kowane nau’in kayan Meta ta hanyar da zai sa su zama mafi mahimmanci ko fitacciyar sigar da aka ƙirƙira.
    • Yin gyara ga nau’in kayayyakin Meta ta wata hanya, kamar ta hanyar canza tsari ko launi, ko kuma ta yin amfani da su cikin fasahar hotuna ko zane mai motsi.
  • Goyon bayan nau’in kaya:
    • Nuna alamar amincewa, ba tare da izinin Meta a rubuce ba, goyon baya ko haɗin gwiwa kowace iri daga wani nau’in kayan Meta.
    • Nuna alamar amincewa, ba tare da izinin Meta a rubuce ba, goyon baya ko haɗin gwiwa kowace iri daga wani nau’in kayan Meta (kamar Facebook, Instagram ko WhatsApp), fasaha ko shiri.
  • Nuna yadda ake amfani da wani kaya ta hanyar da:
    • Nuni ne da ba daidai ba game da yadda samfurin yake a yanzu, sigogi, ko kuma yadda kayayyakin ke aiki.
    • Yin gyara ga yadda ake amfani da kaya ta kowace hanya, kamar ƙara ƙarfin fasaha ta musamman, yadda ake amfani ko zane mai motsi.
    • Yana amfani da abubuwan da ke cikin yadda mai amfani ke gani daban-daban ko a kaɗaice
    • Ba ya kwatanta yadda ake amfani da abu a tsakanin na'urar da ya dace kamar wayar hannu ko kwamfuta.
  • Yin amfani da waƙoƙi ko wasu abubuwa ta hanyar da ta saɓa wa yarjejeniyar lasisin waƙoƙin Meta.
  • Yaɗa bidiyon Facebook Watch mallakar Meta ko/kuma wanda Meta kaɗai ke da lasisinsa ba tare da amincewa a rubuce ba.
  • Amfani da haƙƙin mallakar kaya wanda Meta ne ke da iko a kansu ba tare da izini a rubuce ba.
  • Amfani da alamomin kaya masu kama da alamun kamfanin Meta da zai iya rikitar da mutane.
Muna cire:
  • Asusun da suke maimaita saɓa wa wannan dokar, ciki har da ƙirƙirar sababbin asusu bayan an cire su.
Muna amincewa da abubuwan da ke amfani da haƙƙin mallakar kaya wanda Meta ne ya mallaka ko yake da lasisi ta hanya da ke:
Ƙwarewar mai amfani da kaya
Duba wasu misalai na yadda ɗabbaƙa doka take ga mutanen da suke kan Facebook, kamar: yadda zai kasance wajen kai rahoton abin da kake ganin bai kamata ya kasance a Facebook ba, a faɗa maka cewa ka karya dokar Tsarin Rayuwar Al'ummarmu da kuma ganin allon gargaɗi a kan wani bayani.
Lura: A kullum muna ƙara ingantawa, saboda haka ta yiwu abin da ka gani a nan tsoho ne idan aka kwatanta shi da abin da muke amfani da shi a yanzu.
KWAREWAR MAI AMFANI
Kai rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Sadarwa bayan rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Kwarewar sauke abu
KWAREWAR MAI AMFANI
Allunan gargaɗi
Ɗabbaƙa doka
Muna da manufofi iri ɗaya a duk faɗin duniya, ga duk waɗanda ke kan Facebook.
Ma’aikata da ke sake dubawa
Ƙungiyarmu ta duniya da ke ɗauke da masu bita sama da 15,000 suna aiki kowace rana don kare lafiyar mutane a Facebook.
Aiki tare da masu ruwa da tsaki
Ƙwararru daga waje, malamai, ƙungoyoyin da ba na gwamnati ba da masu tsara dokoki suna taimakawa wajen samar da Tsarin Al'ummar Facebook.
Samu taimako wajen amfani da haƙƙin mallaka da lasisin Meta
Sami bayani a kan abin da za ka iya yi idan ka ga wani abu a Facebook da ya saɓa wa Tsarin Al'ummarmu.
Ziyarci Cibiyar Taimakonmu