Haramtattun Bayani, Kayayyaki ko Ayyuka na Gida

Cikakken bayanin doka

CANZA SHIGA
Ra'ayin Doka
Lokacin da masu tsarawa ko ƙungiyoyi gwamnati suka yi imani da cewa bayanai a kan ayyukanmu sun saɓa wa dokar cikin gida, za a iya neman mu taƙaita abubuwan. Haka nan ƙungiyoyi da ba na gwamnati ba da jama’a na iya aika rahotanni da zargin cewa bayanan ba a bisa doka suke ba. Haka kuma muna iya samun umarnin kotu.
Idan muka samu wani rahoto ko umarni, da farko muna sake dubawa bisa ga Tsarin Rayuwar Al'umma Idan muka tantance cewa abun ya saɓa wa manufofinmu, muna cire shi. Idan abu ba saɓa wa manufofinmu ba, bisa ga saɗaukarwarmu a matsayinmu na mambar Ƙungiyar Sadarwa ta Duniya da kuma Manufofin Haƙƙin Ɗan Adam na Kamfaninmu, muna gudanar da bitar doka tare da yin bincike cikin taka tsantsan don tabbatar da ko rahoton ingantacce ne.
A lokutan da muka yi imanin cewa rahotanni ba su da inganci a shari'a, ko sun yi yawa, ko kuma ba su dace da ƙa'idodin haƙƙin ɗan adam na duniya ba, za mu iya neman ƙarin bayani ko kuma ba za mu ɗauki wani mataki ba.
A lokacin da muka ɗauki mataki a kan bayanan mai amfani bisa ga dokokin cikin gida a maimakon na Tsarin Rayuwar Al'ummarmu, muna taƙaita damar shiga abu kawai a cikin ikon da ake zargin ba bisa ƙa'ida ba ne kuma ba ma sanya wasu hukunci ko takaita sigar. Haka kuma muna sanar da mai amfani da kayan da abin ya shafa.
Haka kuma muna wallafa rahotanni da ke bayyana yadda muke tantance rahotanninmu na bayanan da ke karya dokokin cikin gida da lokutan da muke taƙaita dama ga bayanai a waɗannan lokuta, da ake samu a nan.
Ƙwarewar mai amfani da kaya
Duba wasu misalai na yadda ɗabbaƙa doka take ga mutanen da suke kan Facebook, kamar: yadda zai kasance wajen kai rahoton abin da kake ganin bai kamata ya kasance a Facebook ba, a faɗa maka cewa ka karya dokar Tsarin Rayuwar Al'ummarmu da kuma ganin allon gargaɗi a kan wani bayani.
Lura: A kullum muna ƙara ingantawa, saboda haka ta yiwu abin da ka gani a nan tsoho ne idan aka kwatanta shi da abin da muke amfani da shi a yanzu.
KWAREWAR MAI AMFANI
Kai rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Sadarwa bayan rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Kwarewar sauke abu
KWAREWAR MAI AMFANI
Allunan gargaÉ—i
Ɗabbaƙa doka
Muna da manufofi iri É—aya a duk faÉ—in duniya, ga duk waÉ—anda ke kan Facebook.
Ma’aikata da ke sake dubawa
Ƙungiyarmu ta duniya da ke ɗauke da masu bita sama da 15,000 suna aiki kowace rana don kare lafiyar mutane a Facebook.
Aiki tare da masu ruwa da tsaki
Ƙwararru daga waje, malamai, ƙungoyoyin da ba na gwamnati ba da masu tsara dokoki suna taimakawa wajen samar da Tsarin Al'ummar Facebook.
Samu taimako game da haramtattun bayanai, kayayyaki ko ayyuka na gida
Sami bayani a kan abin da za ka iya yi idan ka ga wani abu a Facebook da ya saɓa wa Tsarin Al'ummarmu.
Ziyarci Cibiyar Taimakonmu