Halayyar Yaɗa Abubuwan Ƙarya

Cikakken bayanin doka

CANZA SHIGA
Ra'ayin Doka
Hali mai Mara Gaskiyai yana nufin hanyoyi dabam-dabam na ruɗi masu wuya, da ake yi da sashen dukiya marar gaskiya da mutum ɗaya ko mutane da yawa suke jagoranci, da manufar ruɗin Meta ko jama'armu ko kuma guje wa bin Mu’amalar Al'umma.
Inda masu barazanar gaba ke amfani da bayanan ƙarya don shiga cikin nagartattun sifofin Ɗabi'ar Yaɗa Abubuwan Ƙarya, suna shiga cikin abin da muka ayyana a matsayin Haɗaɗɗiyar Ɗabi'ar Yaɗa Abubuwan Ƙarya da aka Tsara (CIB).
Waɗannan matakan tilastawa da tsari suna aiki ne ba tare da la'akari da abun ciki ko akida ba kuma suna samar da sarari inda mutane za su amince da mutane da al’ummomin da suke hulɗa da su.
Lokacin da muka gano waɗannan hanyoyin sadarwa, muna cire asusun ƙarya, Shafuka, Ƙungiyoyi, ko wasu kadarorin Meta da ke da hannu kai tsaye a cikin aikin. A lokutan da waɗannan mutanen kuma suke ƙirƙira, kula, amfani da, nufa, ko sarrafa Shafuka, Ƙungiyoyi ko al'ummomi waɗanda ke wakiltar halastattun ɓangarori waɗanda ba su da hannu a cikin ɗabi'ar karya doka, za mu iya ɗaukar matakan cire ɗaiɗaikun mutane masu karya dokar amma mu ƙyale mutanen da ba su da hannu da al'ummomin su ci gaba da kasancewa a kan ayyukanmu.
Duk lokacin da zai yiwu, muna raba sakamakon bincikenmu game da hanyoyin sadarwar CIB a cikin Rahotanninmu na Barazanar Gaba, da ake samu a nan. Waɗannan rahoto ba a nufin su ƙunshi dukan sararin samaniya na yin biyayya a ƙarƙashin manufar Halin Ƙarya ba, amma suna taimaka wajen sanar da fahimtar jama'armu game da canjin hali na barazana da muke fuskanta a wannan filin.
Ba ma ba da damar:
Ƙirƙira, amfani, ko iƙirarin amfani da Kayan Aikin Meta na Ƙarya (Asusu, Shafuka, Ƙungiyoyi, da sauransu) domin:
  • Yaudarar Meta ko masu amfani da mu game da ainihin su wanene, ko asalin masu sauraro ko ɓangaren da suke wakilta
  • Domin kaucewa tilasta aiwatarwa ƙarƙashin Tsarin Mu’amalar Al'umma.
  • Yin amfani da tsarin kai ƙarar Meta ba daidai ba don tursasawa, razanawa ko toshe bakin wasu.
Don waɗannan Tsarin Rayuwar Al'umma, muna buƙatar ƙarin bayani da/ko a muhallin da za a tilasta:
Ba ma ba da damar:
  • Ɓangarorin da ke shiga, ko iƙirarin shiga cikin Haɗaɗɗiyar Ɗabi'ar Yaɗa Abubuwan Ƙarya da aka Tsara, wanda aka ayyana a matsayin nagartattun sifofin Ɗabi'ar Yaɗa Abubuwan Ƙarya inda bayanan ƙarya suke da muhimmanci ga aikin da masu gudanarwa suna amfani da hanyoyin gaba don kaucewa ganowa ko su yi kama da na gaske; da
  • Ƙungiyoyi su shiga ciki, ko iƙirarin shiga cikin Katsalandan daga Waje, wanda aka bayyana a matsayin Ɗabi'un Ƙarya da Aka Haɗe inda masu aikin hanyar sadarwa ba su cikin ƙasar da aikin ke nufi ba
  • Gwamnatocin da suke cigaba da toshe kafafen sada zumunta su yi amfani da sassa, hukumomi, da ofisoshin hulɗar jakadancinsu domin ƙaryata yin amfani da ƙarfi ko sha’anonin amfani da ƙarfi a yanayi na farmaki ga hurumin mallaka na wata ƙasar wanda ya saɓawa Siɗira ta 2(4) ta Ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ƙwarewar mai amfani da kaya
Duba wasu misalai na yadda ɗabbaƙa doka take ga mutanen da suke kan Facebook, kamar: yadda zai kasance wajen kai rahoton abin da kake ganin bai kamata ya kasance a Facebook ba, a faɗa maka cewa ka karya dokar Tsarin Rayuwar Al'ummarmu da kuma ganin allon gargaɗi a kan wani bayani.
Lura: A kullum muna ƙara ingantawa, saboda haka ta yiwu abin da ka gani a nan tsoho ne idan aka kwatanta shi da abin da muke amfani da shi a yanzu.
KWAREWAR MAI AMFANI
Kai rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Sadarwa bayan rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Kwarewar sauke abu
KWAREWAR MAI AMFANI
Allunan gargaɗi
Ɗabbaƙa doka
Muna da manufofi iri ɗaya a duk faɗin duniya, ga duk waɗanda ke kan Facebook.
Ma’aikata da ke sake dubawa
Ƙungiyarmu ta duniya da ke ɗauke da masu bita sama da 15,000 suna aiki kowace rana don kare lafiyar mutane a Facebook.
Aiki tare da masu ruwa da tsaki
Ƙwararru daga waje, malamai, ƙungoyoyin da ba na gwamnati ba da masu tsara dokoki suna taimakawa wajen samar da Tsarin Al'ummar Facebook.
Sami taimako a kan ɗabi'ar yaɗa abubuwan ƙarya
Sami bayani a kan abin da za ka iya yi idan ka ga wani abu a Facebook da ya saɓa wa Tsarin Al'ummarmu.
Ziyarci Cibiyar Taimakonmu