Ci Da Gumin Mutane

Cikakken bayanin doka

CANZA SHIGA
Ra'ayin Doka
A ƙoƙarin daƙilewa da hana cutarwa, mukan cire bayanai da ke shirya ko gudanar da cin zarafin mutane, wanda ya haɗa da safarar mutane. Mukan fassara safarar mutane da cewa harka ce da ake hanawa wani mutum ‘yancin na samun riba. Cutarwa ce ta cin moriyar mutane don tilasta musu shiga jima’in neman kuɗi, ƙwadago, ko wasu harkoki ba bisa son ransu ba. Yana dogara ne kan yaudara, nuna ƙarfi da tursasawa, tare da wulaƙantar da mutane ta hanyar hana musu ‘yancinsu yayin da kuma ya ke amfanar wasu ta fuskar tattalin arziki da dukiya.
Safarar mutane faffaɗan abu ne da ya game duniya; zai iya shafar kowane mutum ba tare da la’akari da shekaru, tushen rayuwar mutum, ƙabilanci, jinsi ko wuri ba. Yana faruwa a sigogi masu yawa, kuma kowane yanayin safara zai iya samun matakai daban-daban na bunƙasa. Saboda tursasawa na wannan cin zarafi, waɗanda ake cutarwa ba za su iya amincewa ba.
Yayin da akwai buƙatar mu kula sosai don ka da mu haɗa safarar mutane da fasa-ƙwauri, za a iya alaƙanta su kuma su shiga juna. Majalisar Ɗinkin Duniya ta fassara fasa ƙwaurin mutane da saye ko shirya shiga wata ƙasa a tsakanin iyakokin ƙasashen duniya ta haramtacciyar hanya. Ba tare da buƙatar tursasawa ko amfani da ƙarfi ba, duk da haka za ta haifar da cin moriyar ɗaiɗaikun mutane masu rauni waɗanda suke ƙoƙarin barin ƙasarsu, yawanci saboda neman kyakkyawar rayuwa. Fasa-ƙwaurin mutane laifi ne ga ƙasa, da ke dogaro da tafiye-tafiye, sannan kuma safarar mutane laifi ne ga mutum, da ke dogaro da cin moriyar mutane.
Ƙari a kan bayanan da ke yin suka ko ɗaukaka wayar da kai a game da, ko kai rahoton labarai a kan fataucin mutane ko matsalar fasa-ƙwaurin mutane, mukan bar bayanai ko raba bayanai a game da kiyayewa ta ƙashin kai da kuma ƙetare iyaka, don neman mafaka ko yadda za a bar wata ƙasa.
Kada a aike:
Bayanai, ayyuka ko hulɗa da ke jan hankalin jama’a ga, yake shiryawa ko cin zarafin mutane ta ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyin fataucin ɗan’adam:
  • Fataucin jima’i (duk wani aikin jima’i na kuÉ—i tare da yaro ko duk wani aikin jima’i na kuÉ—i tare da babba da ya Æ™unshi amfani da Æ™arfi, zamba ko tilastawa)
  • Sayar da yara ko haramtaccen riÆ™o
  • Safarar gidan marayu da yawan shaÆ™atawar gidan marayu
  • Auren da aka tilasta (haÉ—i da auren yara)
  • ci da gumin aiki (da ya haÉ—a da aikin Æ™arÆ™ashin bauta)
  • Aikin bauta na gida
  • Fataucin sashenn jikin da ba a sake samar da su da ya haÉ—a da cirewa, bada gudunmuwa, ko sake dashe a yanayi na gudunmuwar sashen jiki ba da ci da gumi ba
  • Laifi da aka tilasta (misali tilasta yin bara, tilasta safarar miyagun Æ™wayoyi)
  • ÆŠaukar sojoji yara
Bayanin da a inda wani mai aikatawa na daban ya jawo hankali don, ya shirya ko ya amfana daga (ta hanyar kuɗi ko saɓanin haka) aikin jima’i na kuɗi
Bayanin da ke tayin samarwa ko gudanar da fasa-ƙwaurin mutane
Bayanin da ke neman a yi ayyukan fasa-ƙwaurin mutane
Muna ba da dama ga bayanin da ke da kariyar wannan dokar yayin da aka wallafa akan yin alla-wadai, ilimantarwa, wayar da kai, ko yanayin kai rahoton labarai.
A karkashin dokokinmu na Cin Zarafin Mutane, masu sake dubawa da tsarinmu na kai tsaye na iya la'akari da alamun halayya iri-iri don taimakawa gano asusun da ke karya doka da kuma daukar mataki a kansu.
  • Za mu iya cire asusu bisa la'akari da tattaunawarsu da wasu asusu masu karya doka, neman ko tattaunawa da abubuwan da ke karya doka, ko zama mamba a cikin al'ummu (misali Ƙungiyoyi) da muka cire saboda karya dokokinmu.
Don waɗannan Tsarin Rayuwar Al'umma, muna buƙatar ƙarin bayani da/ko a muhallin da za a tilasta:
Za mu iya cire bayanan da ke bayar da aiki a wuraren da ake da haɗarin cin zarafin ma'aikata idan hukumar tilasta bin doka, ƙungiyoyin sa-kai na gida, ko wasu amintattun abokan hulɗa suka tabbatar da hakan.
Ƙwarewar mai amfani da kaya
Duba wasu misalai na yadda ɗabbaƙa doka take ga mutanen da suke kan Facebook, kamar: yadda zai kasance wajen kai rahoton abin da kake ganin bai kamata ya kasance a Facebook ba, a faɗa maka cewa ka karya dokar Tsarin Rayuwar Al'ummarmu da kuma ganin allon gargaɗi a kan wani bayani.
Lura: A kullum muna ƙara ingantawa, saboda haka ta yiwu abin da ka gani a nan tsoho ne idan aka kwatanta shi da abin da muke amfani da shi a yanzu.
KWAREWAR MAI AMFANI
Kai rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Sadarwa bayan rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Kwarewar sauke abu
KWAREWAR MAI AMFANI
Allunan gargaÉ—i
Ɗabbaƙa doka
Muna da manufofi iri É—aya a duk faÉ—in duniya, ga duk waÉ—anda ke kan Facebook.
Ma’aikata da ke sake dubawa
Ƙungiyarmu ta duniya da ke ɗauke da masu bita sama da 15,000 suna aiki kowace rana don kare lafiyar mutane a Facebook.
Aiki tare da masu ruwa da tsaki
Ƙwararru daga waje, malamai, ƙungoyoyin da ba na gwamnati ba da masu tsara dokoki suna taimakawa wajen samar da Tsarin Al'ummar Facebook.
Sami taimako a kan ci da gumin mutane
Sami bayani a kan abin da za ka iya yi idan ka ga wani abu a Facebook da ya saɓa wa Tsarin Al'ummarmu.
Ziyarci Cibiyar Taimakonmu