Ɗabiʼar Ƙiyayya

Cikakken bayanin doka

CANZA SHIGA
Ra'ayin Doka
Mun yi amanna cewa mutane kan yi amfani da muryarsu su haɗa cikin sauki yayin da ba s a samun hari a bisa ga wanene su. Wannan ne ya sa ba ma yarda da halayyar nuna ƙiyayya a Facebook, Instagram, ko Threads.
Muna bayyana halayyar nuna ƙiyayya a matsayin kai hari kai tsaye kan mutane — maimakon ra'ayoyi ko cibiyoyi — a kan abin da muke kira halayen da aka kare (PC): launin fata, kabila, asalin ƙasa, naƙasa, alaƙar addini, dangi, yanayin jima'i, jinsi, asalin jinsi, da mummunar cuta. Bugu da ƙari, muna ɗaukar shekaru a matsayin halin da aka kare lokacin da aka ambata tare da wata halin da aka kare. Muna kuma kare 'yan gudun hijira, baƙi, da masu neman mafaka daga hare-hare mafi tsanani (Mataki na 1 a ƙasa), kodayake muna ba da izinin yin tsokaci da sukar manufofin shige da fice. Hakazalika, mukan samar da wasu kariya ga hallaye na marasa kariya kamar sana’a, lokacin da aka ambace su tare da wata kariyar hali. A wasu lokuta, bisa la'akari da wani yanayi na gida, muna ɗaukar wasu kalmomi ko jimloli a matsayin wakilai da ake yawan amfani da su don halayen da aka kare.
Muna cire maganganun cin mutunci, zarge-zargen mummunar ɗabi'a ko laifi, da gugar zana. Muna kuma cire munanan ra'ayoyi, waɗanda muke bayyana a matsayin kwatancen cin mutunci waɗanda aka yi amfani da su a tarihi don kai hari, tsoratarwa, ko keɓe wasu ƙungiyoyi, kuma waɗanda galibi ana haɗa su da rikici a zahiri. A ƙarshe, muna cire zage-zage masu tsanani, kalamai na raini ko ƙyama, la'ana, da kiraye-kirayen kebancewa ko rarrabewa yayin da ake hari kan mutane bisa halayen da aka kare. Muna raba wannan magana zuwa matakai biyu na tsanani, wanda aka bayyana a ƙasa.
Mun gane cewa a wasu lokuta mutane suna raba bayanai da suka haɗa da gugar zana ko maganar wani don yin Allah wadai da maganar ko bayar da rahoto a kai. A wasu lamuran, zancen, da ya haɗa da ɓatanci, da a wata fuskar zai iya saɓa wa ƙa’idojinmu ana iya amfani da shi ta ambata da kai ko ta hanyar ƙarfafawa. Muna ba da izinin irin wannan magana inda manufar mai magana ta bayyana a sarari. Idan ba a fahimci niyyar ba, za mu iya cire ƙunshiyar.
A wasu lokuta, mutane suna amfani da harshen kebance jima'i ko jinsi yayin tattauna damar shiga wuraren da galibi siffa ko jinsi ke iyakance su, kamar samun damar shiga banɗakuna, wasu makarantu, wasu rundunonin soji, tilasta bin doka, ko ayyukan koyarwa, da ƙungiyoyin lafiya ko tallafi. A wasu lokuta, suna yin kira don a keɓance ko amfani da harshen zagi a cikin mahallin tattauna batutuwan siyasa ko addini, kamar lokacin tattauna haƙƙin masu canza jinsi, shige da fice, ko luwaɗi. A ƙarshe, a wasu lokuta mutane suna tsine wa jinsi a cikin yanayin rabuwar soyayya. An tsara manufofinmu don ba da damar yin irin waɗannan maganganu.
Kada a aike:
Mataki na 1
Bayanai da ke hari kan wani mutum ko ƙungiyar mutane (sai dai ƙungiyoyin da aka bayyana a matsayin waɗanda suka aikata laifukan tashin hankali ko na jima'i ko kuma waɗanda ke wakiltar ƙasa da rabin ƙungiya) bisa la'akari da sifofin da aka ambata a baya ko matsayin shige da fice a rubuce ko a gani da:
  • Kalamai na cin mutunci a cikin siffar kwatance ko haɗa dabbobi, ƙwayoyin cuta, ko wasu nau'ikan rayuwa waɗanda ba mutane ba, har da:
    • Ƙwari (da suka haɗa amma bai taƙaita ba ga: kyankyasai da fari)
    • Dabbobi gaba ɗaya ko takamaiman nau'ikan dabbobi waɗanda a al'adance ake ganin ƙanana (ya haɗa da amma bai taƙaita ga: Baƙaƙen mutane da birrai ko halittu masu kama da birrai; Al’ummar Yahudawa da ɓeraye; Al’ummar musulmi da aladu; Mutanen Meziko da tana)
    • Bakteriya, bairos, ko maikirobs
    • Ƙasƙanci (ciki har da amma ba'a iyakance ga: dabbobi, aljanu, dodanni)
  • Zarge-zargen munanan ɗabi'u da laifuffuka:
    • Masu cin zarafin jima'i da masu lalata yara (ciki har da amma ba'a iyakance ga: Mutane Musulmi masu yin jima’i da awaki ko aladu)
    • Masu aikata laifuka masu tsanani (ciki har da amma ba'a iyakance ga: 'yan ta'adda, masu kisan kai)
  • Kira da fatan awkuwar waɗannan cututtuka (ana magance barazana mai tsanani ko takamaimai da kiraye-kirayen yin tashin hankali a ƙarƙashin manufarmu ta Rikici da Zuga):
    • Kamuwa da cuta
    • Fuskantar wani bala'i
    • Yi wa kai-rauni ko kisan kai
    • Mutuwa ba tare da wanda ya aikata ko hanya ba
    • Haɗari da sauran cututtukan da ke haifar da su ko dai ba tare da wanda ya aikata ba ko kuma ta hanyar wani abin bauta
  • Mummunan ra'ayoyin da aka saba danganta su da tsoratarwa ko tashin hankali, kamar Baƙar Fuska; Musun kisan kiyashi; iƙirarin cewa Yahudawa ne ke kula da cibiyoyin kuɗi, siyasa, ko kafofin watsa labarai; nassoshi ga Dalits a matsayin ma'aikata masu ƙasƙanci; da kwatanta Baƙar fata da kayan aikin gona.
  • Yin izgilanci ga tsari, sha’anoni ko waɗanda aka aikatawa laifin ƙiyayya idan ba a nuna mutum na gaske a hoton ba.
  • Yin ba'a ga mutane saboda suna da ko fama da wata cuta.
  • Bayanan da ke bayyana ko niyya ga mutane da gugar zana. An bayyana gugar zana a matsayin kalmomin da ke haifar da yanayi na kebancewa da tsoratarwa ga mutane bisa la'akari da wata siffa da aka kare, sau da yawa saboda waɗannan kalmomi suna da alaƙa da wariya ta tarihi, zalunci, da tashin hankali.
Mataki na 2
Bayanan da ke hari kan wani mutum ko ƙungiyar mutane bisa la'akari da sifofinsu da aka kare (a rubuce ko a gani) tare da:
  • Kira ko goyon baya ga keɓewa ko rarrabewa ko kalamai na nufin keɓewa ko rarrabewa, wanda aka bayyana a matsayin:
    • Keɓewa gaba ɗaya, wanda ke nufin yin kira don keɓewa ko rarrabewa gaba ɗaya, kamar "Ba a yarda da X ba"
    • Wariyar siyasa, wanda ke nufin hana haƙƙin shiga harkokin siyasa ko yin jayayya don ɗaurin kurkuku ko hana haƙƙin siyasa.
    • Wariyar tattalin arziƙi, wanda ke nufin hana samun damar haƙƙin tattalin arziƙi da takaice shiga cikin kasuwar aiki. Muna ba da izinin bayanai da ke jayayya don iyakokin jinsi na aikin soja, tilasta bin doka, da ayyukan koyarwa. Muna kuma ba da izinin irin wannan bayani bisa la'akari da yanayin jima'i, lokacin da bayanan suka dogara da imanin addini.
    • Ware jama'a, wanda ke nufin abubuwa kamar hana samun damar shiga wurare (na zahiri da na intanet) da ayyukan zamantakewa, sai dai don keɓance jima'i ko jinsi daga wuraren da aka saba iyakance su ta hanyar jima'i ko jinsi, kamar banɗakuna, wasanni da wasannin motsa jiki, ƙungiyoyin lafiya da tallafi, da wasu makarantu.
  • Zage-zage, har da waɗanda ke game da:
    • Hali, har da amma ba'a iyakance ga zargin tsoro, rashin gaskiya, aikata laifi na asali, da lalata ko wasu lalata na jima'i.
    • Halayen hankali, har da amma ba'a iyakance ga zargin wauta, iyawar hankali, da tabin hankali, da kwatancen da ba a tallafa ba tsakanin ƙungiyoyin PC bisa la'akari da iyawar hankali. Muna ba da izinin zargin tabin hankali ko rashin daidaituwa lokacin da aka dogara da jinsi ko yanayin jima'i, idan aka yi la'akari da maganganun siyasa da na addini game da canza jinsi da luwadi da kuma yawan amfani da kalmomi kamar "mai ban mamaki" ba tare da tsanani ba.
    • Sauran wurare, har da amma ba'a iyakance ga zargin rashin daraja, rashin amfani, rashin kyau, datti.
  • Kalamai da ke nuna cewa wanda aka yi niyya yana haifar da rashin lafiya, har da amma ba'a iyakance ga "saka ni amai." ba
  • Tsinuwar da aka nufi, sai ban da wasu la'ana bisa jinsi a cikin yanayin rabuwar soyayya, wanda aka ayyana da cewa:
    • Nufin amfani da "tsinuwa" ko bambancin "tsinuwa" da nufin zagi, kamar "Ƙaniyar [Siffar da Aka Kare]!"
    • Kalmomi ko zantuka da ke kira a haɗu don yin ayyukan jima’i, ko taɓa al’aura, dubura, kashi ko fitsari, da ya haɗa da amma bai taƙaita ba ga: tsotsi azzakarina, sumbaci ɗuwaiwaina, ci kashi.
Don waɗannan Tsarin Rayuwar Al'umma, muna buƙatar ƙarin bayani da/ko a muhallin da za a tilasta:
Kada a aike:
  • Bayanin da a bayyane yake samar da ko tayin samar da kayayyaki ko ayyukan da suke nufin canja daidaitawar jima’in mutane ko shaidar gane jinsi.
  • Bayanin da ke cin zarafin dabaru, cibiyoyi, ra’ayoyi, ayyukoki, ko imani da ta danganta da kariyr hallaye, wanda zasu iya haifar da tsananin cutarwa ta jiki, tsoratrwa ko nuna bambanci ga mutane masu alaƙa da wancan halin da aka kare. Meta yana duba wasu jerin alamomi domin tabbatar da ko akwai wata barazana ta cutarwa a cikin bayanin. Waɗannan sun haɗa da amma ba su taƙaita ba ga: bayanin da zai iya haifar da tsananin tashin hankali ko tsoratarwa; ko akwai lokacin ƙara tashin hankali kamar zabe ko rikicin da ke faruwa; da kuma ko akwai wani tarihin afkuwar tashin hankali kwana nan a kan rukunin da aka kare. A wasu lamuran, haka kuma za mu iya la’akari da cewa ko mai maganar wani fitaccen mutum ne ko yana riƙe da muƙami.
A wasu lamuran, za mu ba da izinin bayanin da wataƙila ya saɓawa Tsarin Al’umma lokacin da aka tabbatar cewa bayanin na ba’a ne. Za a ba da izinin bayani ne kawai idan abubuwan da suka saɓa bayani ana juyar da su zuwa ba’a ne ko danganta su da wani abu ko wani mutum daban domin yi musu ba'a ko suka su.
Lura: Idan kai mai amfani ne na Tarayyar Turai, kuma kana ganin bayanan da ka yi imanin sun keta dokokin kalaman ƙiyayya a cikin ƙasarka, za ka iya miƙa buƙatar cirewa ta doka zuwa Facebook ko Instagram.
Ƙwarewar mai amfani da kaya
Duba wasu misalai na yadda ɗabbaƙa doka take ga mutanen da suke kan Facebook, kamar: yadda zai kasance wajen kai rahoton abin da kake ganin bai kamata ya kasance a Facebook ba, a faɗa maka cewa ka karya dokar Tsarin Rayuwar Al'ummarmu da kuma ganin allon gargaɗi a kan wani bayani.
Lura: A kullum muna ƙara ingantawa, saboda haka ta yiwu abin da ka gani a nan tsoho ne idan aka kwatanta shi da abin da muke amfani da shi a yanzu.
KWAREWAR MAI AMFANI
Kai rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Sadarwa bayan rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Kwarewar sauke abu
KWAREWAR MAI AMFANI
Allunan gargaɗi
Bayanai
Duba sabon bayani game da Rahoton Tilasta Bin Tsarin Rayuwar Al'umma
Ɗabbaƙa doka
Muna da manufofi iri ɗaya a duk faɗin duniya, ga duk waɗanda ke kan Facebook.
Ma’aikata da ke sake dubawa
Ƙungiyarmu ta duniya da ke ɗauke da masu bita sama da 15,000 suna aiki kowace rana don kare lafiyar mutane a Facebook.
Aiki tare da masu ruwa da tsaki
Ƙwararru daga waje, malamai, ƙungoyoyin da ba na gwamnati ba da masu tsara dokoki suna taimakawa wajen samar da Tsarin Al'ummar Facebook.
Samu taimako dangane da halayyar nuna ƙiyayya
Sami bayani a kan abin da za ka iya yi idan ka ga wani abu a Facebook da ya saɓa wa Tsarin Al'ummarmu.
Ziyarci Cibiyar Taimakonmu