Ƙungiyoyi da Ɗaiɗaikun Mutane Masu Haɗari
Cikakken bayanin doka
CANZA SHIGA
Yau
19 Mar, 2026
8 Fab, 2024
29 Dis, 2023
29 Agu, 2023
27 Afrilu, 2023
23 Dis, 2021
24 Nuw, 2021
15 Okt, 2021
26 Agu, 2021
23 Yun, 2021
22 Okt, 2020
27 Agu, 2020
27 Fab, 2020
10 Okt, 2019
27 Sat, 2019
28 Dis, 2018
Ra'ayin Doka
A ƙoƙarin hanawa da daƙile cutarwa ta duniya a zahiri, ba ma barin ƙungiyoyi ko ɗaiɗaikun mutane da ke ayyana manufar tashin hankali ko suke kan aiwatar da tashin hankali su kasance a kan dandalinmu. Mukan tantance waɗannan ƙungiyoyi ta hanyar halayyarsu a wajen intanet a kai da kuma wjen intanet, mafi muhimmanci ma, kusancinsu da tarzoma. Ƙarƙashin wannan manufa, mukan ayyana ɗaiɗaikun mutane, ƙungiyoyi, da haɗakar mutane. Waɗannan ayyanawa sun kasu zuwa matakai uku da ke nuna matsayin tilasta aiki da bayanai, inda Mataki na 1 ya samar da mafi tsananin tilastawa saboda mun yarda cewa waɗannan ƙungiyoyi suna da dangantaka ta kai tsaye a cutarwa ba ta kan intanet ba.
Mataki na 1 yana maida hankali ne kan ƙungiyoyin da suke aikata cutarwa ba ta kan intanet ba - da ya haɗa da shiryawa ko neman a aiwatar da tashin hankali kan farar hula, cigaba da wulaƙantawa ko neman cutarwa a kan mutane bisa ga siffofin da aka kare, ko aikata ayyukan laifi. Mataki na 1 ya haɗa da ƙungiyoyin nuna ƙiyayya; ƙungiyoyin aikata laifuka, da suka haɗa da waɗanda gwamnatin Amurka ta ayyana su a matsayin Jagororin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Na Musamman Da Aka Ayyana wato SDNTKs; da kuma ƙungiyoyin ‘yan ta’adda, da suka haɗa da ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane da gwamnatin Amurka ta ayyana su a matsayin Ƙungiyoyin ‘Yan ta’adda na Ƙasashen Waje, FTOs ko ‘Yan Ta’addan Duniya Da Aka Ayyana Na Musamman, SDGTs. Mukan cire Kwarzantawa, Goyon baya, da kuma Wakilcin Ƙungiyoyin Mataki na 1 tare da shugabanninsu, waɗanda suka kafa su, ko sanannun ‘yan ƙungiya, da manazartar da ba su fahimta ba.
Bugu da ƙari, ba ma barin bayanan da kwarzanta, goyon baya, ko ya wakilci sha’anonin da Meta ya ayyana su a matsayin sha’anonin tashin hankali da suka saɓa - da suka haɗa da hare-haren ‘yan ta’adda, sha’anonin nuna ƙiyayya, tashin hankali da ya shafi ɗimbin jama’a ko yunƙurin aikata tashin hankali da zai shafi ɗimbin jama’a, kisan ƙare-dangi, ko laifukan nuna ƙiyayya. Ba kuma ma barin (1) Kwarzanatwa, Goyon baya, ko Wakilcin masu aikata waɗannan hare-haren; (2) bayanan da mai aikatawa ya samar da suka danganci waɗannan hare-haren; ko (3) hotunan wani na daban da ke nuna lokacin faruwar waɗannan hare-haren akan mutanen da ake gani. Muna cir bayanan da ke Kwarzanta, Goyon baya ko Wakilcin aƙidun da ke haɓaka ƙiyayya, kamar wariyar launin fata da aƙidar farar fata zalla, muna cire manzartar da ba a fahimta ba a waɗannan sha’anona ko aƙidu.
Mataki na 2 ya haɗa da Tsageru da ke haddasa tashintashina a kan wata ƙasa ko sojoji a rikicin da aka gwabza wanda ba a nufi farar fata ba. Har ila yau, ya haɗa da Ƙungiyoyin Tashin hankali waɗanda ke da hannu wajen shirya ko bayar da shawarwari don tashin hankali na gaba amma ba lallai ba ne su shiga tashin hankali har yau. Waɗannan ma ƙungiyoyi ne waɗanda za su iya maimaita aikata karya dokokinmu na Ɗabiʼar Ƙiyayya ko Mutane da Ƙungiyoyi Masu Haɗari a ciki ko waje da dandalin. Mukan cire Kwarzantawa, Kayan Goyon baya, da kuma Wakilcin Ƙungiyoyi, da shugabanninsu, waɗanda suka kafa su, ko sanannun ‘yan ƙungiya.
Mun gane cewa masu amfani za su iya raba ƙunshiya wanda ya haɗa da nassoshi ga ƙayyadaddun ƙungiyoyi masu haɗari da daidaikun mutane a cikin mahallin tattaunawar zamantakewa da siyasa. Wannan ya haɗa da ba da rahoton ƙunshiya, tattaunawa ba tare da tsangwama ko yin Allah wadai da ƙungiyoyi masu haɗari da mutane ko ayyukansu ba.
Rahoton labarai ya haɗa da bayanin da aka yaɗa don a wayar da kai game da sha’anonin gida da na duniya wanda a cikinsa ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane masu hatsari da aka ayyana suke ciki.
- Misali. “Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Al-Shabab ta ɗauki nauyin kai hari a Somaliya”
- Misali. “Tsarin lokaci da sharhin ƙwararru: Yadda harbin a Babbar Kasuwar Buffalo ya faru da kuma abin da mai laifin ya faɗa a kotu”
Tattaunawar ‘yan-ba’ruwanmu ta haɗa da jawaban gaskiya, sharhi, tambayoyi, da sauran bayanin da ba ya bayyana hukunci ga ƙungiyoyi ko ɗaiɗaikun mutane masu haɗari da aka ayyana da kuma halayyarsu.
- Misali. “Al Qaeda tana da ƙarancin barazana a kan ISIS saboda rashin shugabanci da hanyar samun kuɗi”
- Misali. “Anders Breivik misali ne na yadda hanyar tsattsauran ra’ayi zai iya kasancewa mai sarƙaƙiya”
Yin Allah-wadai ya haɗa da ƙin amincewa, baƙin ciki, ƙin yarda, suka, izgilanci, da sauran bayanai marasa kyau game da wata ƙungiya ko mutum mai hatsari da aka ayyana da kuma halayyyarsu.
- Misali. “Raina ya ɓaci da laifin Salvador Ramos. Kalaman alƙalin sun yi matuƙar ratsa ni. Bai kamata a yi masa sassauci a kotu ba”
- Misali. “Har abada ba za a manta da laifukan aifukan Hitler ba. Waɗannan su ne wasu lokuta mafi muni a tarihi”
An tsara manufofinmu ne don su ba da damar waɗannan nau’ikan tattaunawa yayin a lokaci guda kuma suke taƙaice haɗarin samun cutarwa ba ta kan intanet ba. Saboda haka mu kan buƙaci mutane su nuna niyyarsu a bayyane yayin ƙirƙira ko yaɗa waɗannan bayanai. idan niyyar mai amfani tana da sarƙaƙiya ko ba a ganewa, mu kan dauwamar zuwa cire bayanai.
A bisa dokar haƙƙin ɗan adam ta duniya, manufofinmu su kan ba da dama tattaunawa game da haƙƙin ɗan adam na ɗaiɗaikun mutanen da aka ayyana ko mambobin ƙungiyoyi masu haɗari da aka ayyana, sai dai idan bayanin ya ƙunshi wasu kwarzantawa, goyon baya, ko wakilci na ƙungiyoyin da aka ayyana ko wasu saɓawa manufofin, kamar ingizawa a aikata tashin hankali.
Dubi Manufar Haƙƙin Ɗan Adam ta Kamfanidomin ƙarin bayani game da jajircewarmu kan haƙƙoƙin ɗan adam da duniya ta yarda da su.
Muna cire:
Mukan cire kwarzantawa, taimako da wakilcin miyagun ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane daban-daban. Waɗannan tsaruka sun shafi su kansu ƙungiyoyin, harkokinsu, da kuma mambobinsu. Waɗannan tsaruka ba sa haramta neman yin abu cikin lumana domin wasu sakamakon siyasa na musamman.
Kwarzantawa, da aka fassara da kowane ɗaya daga abubuwa na ƙasa:
- Halastawa ko kare ayyukan tashin hankali ko na nuna ƙiyayya na wata ƙungiya da aka ayyana ta hanyar iƙrarin cewa waɗannan ayyuka suna da hujja ta ɗabi’a, siyasa, hankali ko wani dalilin da ke sanya wa a karɓe su ko masu hujja.
- Misali. “Hitler bai aikata laifin komai ba.”
- Bayyanawa ko yin murnar tashin hankali ko ƙiyayya ta ƙungiyar da aka ayyana a matsayin cimma nasara ko cigaba;
- Misali. “Hizbul Mujahideen tana samun nasara a yaƙin ‘yantar da ƙasar Kashmir”
- Wani jawabin burin zamamemba ko jawabin cewa za ka so zama ƙungiyar da aka ayyana ko mai aikata sha’anin tashin hankali da ya saɓa.
- Misali. “Ina ma zan iya shiga ISIS don in kasance cikin Khilafah”
Mukan cire Kwarzantawa na Mataki na 1 da Mataki na 2 da kuma sha’anonin da aka ayyana.
Ga Mataki na 1 sha’anoni, wataƙila mu cire bayanan da ba su da tabbas ko mara tushe idan ba a bayyana manufar mai amfani ba. Wannan ya haɗa da ba'a maras kyau, taken magana ko tabbataccen nassoshi waɗanda ba sa kwarzanta tashin hankali ko ƙiyayyar ƙungiyar da aka keɓe.
Taimako, an bayyana ma’anarsa da:
- Taimako na Kaya
- Duk wani aiki da zai inganta matsayin kuɗi na ƙungiyar da aka keɓe - da ya hada da tara kuɗi zuwa ko nesa da abin da aka keɓance;
- Misali, “A ba da gudunmuwa ga KKK!”
- Duk wani da ke samar da taimakon kaya ga wata ƙungiya ko sha’ani da aka ayyana;
- Misali, “Idan kana son aika wa da kayan taimako zuwa ga Sinaloa Cartel, yi amfani da wannan adireshi.”
- Ɗauka a madadin wata ƙungiya ko sha’ani da aka ayyana;
- Misali, “Idan kuna son yin yaƙi saboda Daular Musulunci, turo min saƙo”
- Sauran Taimako
- Tura bayanai ko dukiya, da suka haɗa da Bayanan Sadarwa, a madadin wata ƙungiya ko sha’ani da aka ayyana
- Misali, ruwaito magana wata ƙungiya ko sha’ani da aka ayyana ba tare da wani jawabi na sukar maganar, yake tattauna wa ba tare da taimako ba, ko kuma ɓangare ne na labarai.
- Yin kira zuwa aikatawa a madadin wata ƙungiya ko sha’ani da aka ayyana;
- Misali. Misali, “Tuntuɓi Sashen Atomwaffen– (XXX) XXX-XXXX"
Mukan cire duk wani Taimako na Mataki na 1 da Taimako na Kaya na Mataki na 2.
Wakilci, da aka fassara da kowane ɗaya daga abubuwa na ƙasa:
- Faɗin cewa kai mamba ne a ƙungiya ko sha’anin da aka ayyana;
- Misali, “Ni babban dragon ne a KKK.”
- Ƙirƙirar wani shafi, Furofayil, Sha'ani, Rukuni, ko wata ƙungiyar Facebook da ta ke ko ake zargin mallakar wata Ƙungiya Da Aka Ayyana ce ko ake gudanarwa a madadin su, ko ta ke ko ake zargin sha'ani ne da aka ayyana.
- Misali, wani Shafi mai suna “Jam’iyyar Nazi ta Amurka.”
Mukan cire Wakilci na Ƙungiyoyin Da Aka Ayyana a Mataki na 1 da 2 da sha’anonin da aka ayyana.
Rabe-rabe da Matakai na Miyagun Ƙungiyoyi
Mataki na 1 Ta'addanci, shiryayyar ƙiyayya, manya-manyan ayyukan laifi, yunƙurin cutar da mutane da dama, cutar da mutane da dama, kisan kai da yawa, da kuma sha’anonin tashin hankali
Ba ma ƙyale ɗaiɗaikun mutane ko ƙungiyoyin da suke aiwatar da shiryayyun al’amuran aikata laifuka, da suka haɗa da waɗanda gwamnatin Amurka ta ayyana su a matsayin Jagororin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Na Musamman Da Aka Ayyana (SDNTKs); da kuma ƙungiyoyin ‘yan ta’adda, da suka haɗa da ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane da gwamnatin Amurka ta ayyana su a matsayin Ƙungiyoyin ‘Yan ta’adda na Ƙasashen Waje (FTOs) ko ‘Yan Ta’addan Duniya Da Aka Ayyana Na Musamman (SDGTs), su kasance a kan dandamalin. Haka kuma ba ma ƙyale wasu mutane su wakilci waɗannan ƙungiyoyi. Ba mu ƙyale shugabanni ko fitattun membobin waɗannan ƙungiyoyi su sami halarta a kan dandali, alamomin da ke wakiltar su don amfani da su a kan dandali, ko abubuwan da ke kwarzanta su ko ayyukansu, da ya hada da nassoshi marasa tabbas game da. Bugu da ƙari, muna cire duk wani taimako ga waɗannan mutane da ƙungiyoyi.
Ba ma barin bayanin da ke kwarzanta, ba da taimako, ko ya ke wakiltar sha’anonin da Meta ya ayyana su a matsayin hare-haren ‘yan ta’adda, sha’anonin nuna ƙiyayya, tashin hankali da ya shafi ɗimbin jama’a ko yunƙurin aikata tashin hankali da zai shafi ɗimbin jama’a, kisan ɗauki ɗaiɗai, laifukan nuna ƙiyayya. ko sha'anonin tashin hankali da suka saɓa. Ba kuma ma barin (1) bayanan da ke kwarzanta, taimakon, ko wakilcin masu aikata waɗannan hare-haren; (2) bayanan da mai aikatawa ya samar da suka danganci waɗannan hare-haren; ko (3) hotunan wani na daban da ke nuna lokacin faruwar waɗannan hare-haren akan mutanen da ake gani.
Ba mu yarda da Kwarzantawa, Taimako, ko Wakilcin ƙayyadaddun akidu masu ƙiyayya ba, da kuma abubuwan da ba su da tabbas game da.
Ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da ɗaiɗaikun mutane, da aka fasara da ƙungiyoyin da ba gwamnati ba:
- Da ke aikata, neman a yi, ko yake bayar da isasshen taimako ga shiryayyun ayyukan tashin hankali da aka yi da manufa.
- Wanda ke haddasawa ko yunƙurin haddasa mutuwa, rauni ko matsananciyar cutarwa ga fararen hulla, ko kowane irin mutum da ba ya cikin rikicin kai tsaye a yanayin faɗa da makamai, da/ko yin gagarumar ɓarna ga dukiyoyi da ya jawo mutuwa, mummunan rauni ko cutarwa ga fararen hula
- Da niyyar tursasawa, tsoratarwa da/ko jawo hankalin wata al’ummar farar hula, gwamnati, ko ƙungiyar ƙasa da ƙasa
- Domin cimma manufar siyasa, addini, ko ta aƙida.
Ƙungiyar Ƙiyayya, an fassara ta a matsayin ƙungiya ko mutum da ke yaɗawa da ƙarfafa nuna ƙiyayya akan wasu bisa ga siffofinsu da aka kare. Ana gane ayyukan ƙungiyar ne ta aƙalla wasu daga ɗabi’u masu zuwa:
- Tashin hankali, kalaman tsoratarwa, ko nau’ikan cusgunawa masu haɗari da ake nufar mutane bisa ga siffofinsu da aka kare;
- Maimaita amfani da kalaman ƙiyayya;
- Wakilcin Aƙidun Ƙiyayya ko wasu Ƙungiyoyin Ƙiyayya da aka ayyana, da/ko
- Kwarzantawa ko Taimako na wasu Ƙungiyoyin Ƙiyayya Aƙidun Ƙiyayya da aka ayyana.
Ƙungiyoyin Masu Aikata Laifuka, da aka fassara da tarayyar mutane uku ko fiye da haka da:
- suka yi tarayya ƙarƙashin suna, launi, nuni da hannu ko wasu sanannun alamomi; da
- ta shiga aikata ko yin barazanar shiga aikata laifi kamar kisan kai, safarar miyagun ƙwayoyi, ko yin garkuwa da mutane.
Tashin Hankalin da ya Shafi Ɗimbin Mutane da Kisan Kai Da Yawa
- Mukan yi la'aƙari sha’ani a matsayin tashin hankalin da ya shafi ɗimbin mutane ko yunkurin tashin hankalin da ya shafi ɗimbin mutane idan ya shafi mutane uku ko fiye a faruwa ɗaya, da aka fassara da mutuwa ko matsanancin rauni. Dukkan mutumin da ya aikata irin wannan farmaki ana ɗaukar sa a matsayin mai aikatawa ko mai yunƙurin aikata tashin hankalin da ya shafi ɗimbin mutane.
- Mukan ɗauki dukkan mutumin da ya aikata kisan kai biyu ko fiye da haka a faruwar lamura ko wurare masu yawa a matsayin mai kisan kai da yawa.
Aƙidun Nuna Ƙiyayya
- Yayin da ayyanawar da mu ke yi wa ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane tana maida hankali ne kan halayya, haka kuma mu kan yarda cewa akwai wasu aƙidu da abubuwan da aka yi imani waɗanda suke ɗamfare da tashin hankali da yunƙurin jawo mutane su amsa kiran aikata tashin hankali ko ware wasu a bisa siffofinsu da aka kare. A waɗannan lamura, mu kan ayyana ita aƙidar sannan mu cire bayanin da ke taimakon wannan aƙida daga dandamalinmu. Waɗannan aƙidu sun haɗa da:
- Nazi
- Aƙidar Farar Fata Zalla
- Kishin Ƙasar Farar Fata
- Aƙidar Wariyar Farar Fata
- Mukan cire Kwarzantawa, Taimako, da Wakilcin waɗannan aƙidu, kuma mu kan cire ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi da ke danganta kansu da ɗaya ko fiye da haka na waɗannan aƙidun ƙiyayyar.
Mataki na 2: Tsageru Masu Tashintashina da Rikici Da Ya Hada da Kungiyoyi
Ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane da Meta ya ayyana a matsayin ‘Yan Tashin Hankali Da Ba Gwamnati Ba ko Ƙungiyoyi Masu Haddasa tahin hankali an haramta musu kasancewa a kan Facebook, ko wasu su kasance a madadinsu. Kamar yadda wadannan al’ummomi suka fada cikin tashin hankali, a kan hukuma ko sojoji a rikicin yaki na (Tsageru Masu Tashintashina) ko suna shirin ko neman samar da wasu sharudda don rikici na gaba (Tashin hankali da ya Hada da Kungiyoyi), ba a yarda taimakon kaya na wadannan kungiyoyi ba. Za mu cire kwarzantawa na wadannan kungiyoyi.
‘Yan Tashin Hankali Da Ba Gwamnati Ba, da aka fassara da duk wata ƙungiyar da ba gwamnati ba da:
- Yana shiga cikin wani tsari mai ma'ana da tsare-tsare na munanan tashe-tashen hankula da suka shafi gwamnati, sojoji ko wasu kungiyoyi masu dauke da makamai da ke taka rawa kai tsaye a cikin fadace-fadacen da ake fama da shi a halin da ake ciki na fadace-fadacen da ake yi da makami, kuma ba da ganganci da kuma fito-na-fito da farar hula da tashin hankali ba; DA/KO
- Yana hana al'ummomi damar samun muhimman ababen more rayuwa ko albarkatun ƙasa; DA/KO
- Yana shiga cikin wani nau'in hare-haren da aka yi niyya don kawo babbar barna ga ababen more rayuwa waɗanda ba su da alaƙa da mutuwa, mummunan rauni ko cutarwa ga farar hula.
Tashin hankali da ya hada da Kungiyoyia bayyana su kamar haka:
Tashin hankali da ya Hada da Kungiya (Baki Daya) wasu tsageru ne da ke:
- Tana da, a matsayin manufarta da ta bayyana ko aikin da take son yi don samar da, ta hanyar rikici, aikin tilastawa na gwamnati da ba a amince da shi ba (kamar 'yan sanda, sojoji, shige da fice) a matsayin, ko a ƙari kan gwamnati da kanta; ko don tarwatsa aikin tilastawa na gwamnati ta hanyar rikici;
- Ta ɗauki babban mataki game da wannan manufa da aka bayyana a dandalan Meta; kuma
- Ta shiga cikin lokuta da yawa na yin barazana ko zuga a yi mummunan rikici (a kan intanet ko a wajen intanet);
A Kungiyar Kiyayya da aka Haramta kungiyar tsageru ce da ke:
- Da ke aikata ɗabi’ar ƙiyayya ko zancen baki, amma ba su kai matsayin ƙungiyar Mataki na 1 ba, saboda ba su aikata ko a bayyane suka nemi a yi tashin hankali ba, ko saboda suna da ƙarancin dangantaka da ƙungiyoyi ko alƙaluman da aka ayyana a baya ba.
Don waɗannan Tsarin Rayuwar Al'umma, muna buƙatar ƙarin bayani da/ko a muhallin da za a tilasta:
- A wasu lamuran, za mu ba da izinin bayanin da wataƙila ya saɓawa Tsarin Al’umma lokacin da aka tabbatar cewa bayanin na ba’a ne. Za a ba da izinin bayani ne kawai idan abubuwan da suka saɓa bayani ana juyar da su zuwa ba’a ne ko danganta su da wani abu ko wani mutum daban domin yi musu ba'a ko suka su.
Ƙwarewar mai amfani da kaya
Duba wasu misalai na yadda ɗabbaƙa doka take ga mutanen da suke kan Facebook, kamar: yadda zai kasance wajen kai rahoton abin da kake ganin bai kamata ya kasance a Facebook ba, a faɗa maka cewa ka karya dokar Tsarin Rayuwar Al'ummarmu da kuma ganin allon gargaɗi a kan wani bayani.
Lura: A kullum muna ƙara ingantawa, saboda haka ta yiwu abin da ka gani a nan tsoho ne idan aka kwatanta shi da abin da muke amfani da shi a yanzu.
KWAREWAR MAI AMFANI
Kai rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Sadarwa bayan rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Kwarewar sauke abu
KWAREWAR MAI AMFANI
Allunan gargaɗi
Bayanai
Duba sabon bayani game da Rahoton Tilasta Bin Tsarin Rayuwar Al'umma
Ɗabbaƙa doka
Muna da manufofi iri ɗaya a duk faɗin duniya, ga duk waɗanda ke kan Facebook.
Ma’aikata da ke sake dubawa
Ƙungiyarmu ta duniya da ke ɗauke da masu bita sama da 15,000 suna aiki kowace rana don kare lafiyar mutane a Facebook.
Aiki tare da masu ruwa da tsaki
Ƙwararru daga waje, malamai, ƙungoyoyin da ba na gwamnati ba da masu tsara dokoki suna taimakawa wajen samar da Tsarin Al'ummar Facebook.
Sami taimako a kan mutane da ƙungiyoyi masu haɗari
Sami bayani a kan abin da za ka iya yi idan ka ga wani abu a Facebook da ya saɓa wa Tsarin Al'ummarmu.
Ziyarci Cibiyar Taimakonmu