Ci Da Gumin Yara Ta Hanyar Jima’i, da Cin Zarafi, da Nuna Tsiraici

Cikakken bayanin doka

CANZA SHIGA
Ra'ayin Doka
Ba ma barin bayanai ko ayyukan da suke yin amfani da yara ta hanyar jima’i ko jefa su cikin haɗari. Yayin da muka gane wani lamarin amfani da yara, mu kan kai rahotonsa ga Cibiyar Kula da Yara Da Suka Ɓata da Waɗanda Aka Ci Zarafinsu ta Ƙasa (NCMEC), domin cika umarnin dokar da ke aiki. Mun san cewa wasu lokutan mutane suna yaɗa hotunan tsiraici na ‘ya’yansu da kyakkyawar niyya; sai dai kuma, gabaɗaya mukan cire waɗannan hotuna saboda za su iya jawo cin zarafi daga wasu da kuma taimakawa a kaucewa yiwuwar wasu mutane su sake amfani da hotunan ko sarrafa su ta mummunar hanya.
Haka kuma muna aiki tare da ƙwararru daga waje, da suka haɗa da Hukumar Ba Da Shawarwarin Kariya ta Meta, domin tattaunawa da bunƙasa dokokinmu da tilasta aiki da su a al’amuran kariya a kan intanet, musamman dangane da yara. Sami ƙarin bayani game da fasahar da muke amfani da ita wajen yaƙar cin zarafin yara.
Kada a aike:
Yin lalata da ƙananan yara
Bayani, aiki ko tattaunawa da ke barazana, nunawa, yabon, goyon bayan, samar da bayanan jagora ga, yin jawaban bayyana niyya, amincewa da shiga aikata ko yaɗa mahaɗai na yin lalata da ƙananan yara (da ya haɗa da ƙananan yara na gaske, yara ko jarirai ko abubuwan da ba na gaske ba tare da kamannin mutum, kamar a cikin fasaha, abubuwan da aka samar da Fashar AI, haruffan almara, tsana, da sauransu). Wannan ya haɗa da amma bai taƙaita ga:
  • Yin jima’i
    • Saduwar jima’i a bayyane ko jima’i na baki, da aka fassara da shigar da baki ko al’aura ko taɓa al’aura ko duburar wani mutum, inda aƙalla ake ganin tsiraicin al’aurar ko dubarar mutum.
    • Ƙwatancin saduwar jima’i ko jima’i na baki, da suka haɗa da lokacin babu makawa sai an yi shafa ko ba a gani kai tsaye.
    • Motsa sha’awar al’aura da dubura, da ya haɗa da lokacin babu makawa sai an aikata ko ba a gani kai tsaye.
    • Kowane daga abubuwan sama da ya haɗa da dabba.
  • Yara da suke da masaniyar jima’i, da ya haɗa da amma bai taƙaita ga:
    • Kame kai
    • Alamun tashin sha’awa
    • Mayar da hankali ga al’aura ko dubura
    • Halartar babban da sha’awarsa ta motsa
    • Kasancewar kayan wasan jima'i ko amfani da kowane abu don motsa jiki ko gamsuwa, ko cin zarafin jima’i
    • Tufafin motsa sha’awa
    • Yin tsirara
    • Muhallin da aka gabatar (misali, akan gado) ko wanda ƙwararre ya ɗauka (inganci/fitar hoto/kusurwoyi)
    • Sumbatar baki-a-buɗe
    • Ƙarfafa nonon mutum ko matse nono na mace (SAI a yanayi na shayarwa).
    • Bayyanar abubuwan da ake samu bayan yin jima’i
  • Abubuwan da suka shafi yara a cikin muhallin jima'i
  • Bayanin da ke goyon baya, yaɗawa, neman a yi ko ƙarfafa gwiwar shiga aikata lalata da yara sai dai in ya tattauna matsayin tsaka tsaki a yanayi na kiwon lafiya
  • Bayanin da yake bayyana ko yin izgili ga waɗanda ake zargin lalata da ƙananan yara ta shafe su ta suna ko hoto
Roƙo
Ƙunshiyar da ke neman abubuwa na jima'i ko ayyukan da ke nunawa ko haɗa yara, wanda aka ayyana a zaman:
  • Kayan Yin jima’i Da Ƙananan Yara
  • Hoton tsiraicin yara na gaske ko wanda ba na gaske ba
  • Hoton lalata da yara na gaske ko na wanda ba na gaske ba
Yin mu’amala da yara ta hanyar da ba ta dace ba
Bayanin da ke ƙullawa ko gudanar da hulɗa da yara ta hanyar da ba ta dace ba, kamar:
  • Roƙo, shiryawa ko tsara yin jima'i da ƙananan yara
  • Jawo hankalin ƙananan yara don yin jima'i ta hanyar tattaunawa ta batsa ko bayarwa, nunawa, samu ko neman kayan batsa zuwa ga ƙananan yara ko daga gare su, ta hanyar nuna tsiraici da gangan ko a saƙonnin sirri
  • Yin hirar kalaman jima’i a bayyane ta hanyar saƙonnin sirri ga yara
  • Samu ko tambayar kayan jima’i daga wurin yara ta hanyar saƙonnin sirri
Hoton kusanci na cin moriya da barazanar yaɗa hoto na tsiraici
Ƙunshiyar da ke yunƙurin yin amfani da ƙananan yara na gaske ta hanyar:
  • Amfani da tursasawa a karɓi kuɗi, alfarma, ko hoton tsiraici da barazanar fallasa hoton mara gaskiya tsiraici ko bayanan sirrin su
  • Yaɗawa, yin barazana ko bayyana niyyar yaɗa hirar jima’i ta sirri ko hoton tsiraici na gaske ko ba na gaske ba
Mayar da yara ababen yin jima’i
  • Bayanin da ya haɗa da (hotuna, bidiyo, aikin fasaha na zahiri, bayanan cikin na’ura, da kuma kalmomin baki) da ke koyawa yara harkar jima’i ga yara na gaske ko ba na gaske ba
  • Rukunoni, Shafuka da furofayil da aka samar don koya wa yara harkar jima’i na gaske ko ba na gaske ba
Tsiraicin yara
Bayanin da ke nuna tsiraicin yara na gaske ko ba na gaske ba a inda aka fassara tsiraici da:
  • Kusantar al’aurar yara na gaske ba na gaske ba
  • Jarirai tsirara a zahiri na gaske ko ba na gaske ba, da ke nuna:
    • Bayyanar al’aura, ko da kuwa an rufe da tufafi mai shara-shara
    • Bayyanar dubura da/ko kallon kusan buɗaɗɗen ɗuwaiwai
  • Ƙananan yara tsirara a zahiri na gaske ko ba na gaske ba, da ke nuna:
    • Bayyanar dubura (da ya haɗa da al’aurar da kawai gashin-gaba ne ya rufe ta ko tufafi mai shara-shara)
    • Bayyanar dubura da/ko kallon kusan buɗaɗɗen ɗuwaiwai
    • Nonon mace da ke buɗe
    • Babu tufafi daga wuya zuwa guiwa - koda kuwa ba a nuna al’aura ko nonon mace ba
  • Sai dai idan hoton da ba na gaskiya ba na lafiya ne ko kuma nunin tsiraicin yara a cikin fasahar kalma ta gaske amma ba na lalata ba.
Cin zarafin yara ba ta hanyar jima'i ba
Bidiyo ko hotunan da ke nuna ainihin cin zarafin yara ba tare da jima'i ba ko da kuwa raba niyya, sai dai idan hotunan daga zane-zane na duniya ne, zane-zane, fina-finai ko wasanni na bidiyo.
Bayanin da ke yabon, goyon bayan, yaɗawa, neman a yi, samar da bayanan jagora ga ko ya ke ƙarfafa guiwa a aikata cin zarafin yara ba ta hanyar jima'i ba
Baya ga cire asusu da suka keta manufofinmu na Ci Da Gumin Yara Ta Hanyar Jima’i da Cin Zarafi da Nuna Tsiraici (CSEAN), masu bitar da tsari mai sarrafa kansa na la’akari da kadadar sigina domin taiamakwa wajen daƙile mu’amala marar kyau ko mai cutarwa.
  • Za mu iya kashe asusu ko mu ƙayyade damar shiga kayayyaki da sigogi (misali, damar bin wasu asusu) ga manya bisa ga tattaunawarsu da wasu asusu, bincike ko tattaunawa da abun da ke karya doka (misali, son abu ko adana shi), ko zama mamba a cikin al'umma (misali, Ƙungiyoyi) da muka cire saboda karya dokokinmu.
Ga wannan bayani, mukan haɗa da allon gargaɗi domin mutane su san cewa bayanin zai iya kasancewa tada hankali sannan mu taƙaita damar gani ga manya ‘yan tsakanin shekaru goma-sha-takwas zuwa sama:
  • Bidiyo ko hotunan da ke nuna jami’an ‘yansanda ko sojoji suna aikata cin zarafin yara ba ta hanyar jima'i ba
  • Bidiyo ko hoton da ba na cin zarafin yara ta hanyar jima'i ba, yayin da hukumar kula da doka, hukumomin ba da kariya ga yara, ko amintattun abokan hulɗar kariya suka buƙaci cewa mu ƙyale bayanin akan dandamali da bayyananniyar manufa ta kuɓutar da yaro
Ga wannan bayanin, mukan haɗa da fuskar waya ta taka-tsantsam domin mutane su san cewa bayanin zai iya tada hankalin wasu:
  • Bidiyo ko hotuna na tsoma yaro a cikin ruwa a yanayi na ayyukan bautar addini
Don waɗannan Tsarin Rayuwar Al'umma, muna buƙatar ƙarin bayani da/ko a muhallin da za a tilasta:
Ga wannan bayanin, mukan haɗa da wata alama domin mutane su san cewa bayanin zai iya kasancewa na taka tsantsam:
  • Hotunan da kamfanin watsa labarai ya wallafa da ke nuna tsiraicin yara a yanayi na fari, kisan ƙare dangi, laifukan yaƙi, laifi ga bil’adama, sai dai in yana haɗe da take da ya ke saɓawa ko aka yaɗa a yanayi na saɓawa, a inda aka cire bayanin
Za mu iya cire hoton da ke nuna bayan faruwar cin zarafin yara ba ta hanyar jima'i ba lokacin da abokan hulɗar kafafen watsa labarai, ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba ko wasu amintattun abokan hulɗar suka ba da rahoton sa.
Za mu iya cire ƙunshiya wanda ke gano wadanda ake zargi da cin zarafin yara ta hanyar wasu hanyoyi daban-daban ban da suna ko hoto idan ƙunshiya ya ƙunshi bayanin da zai iya kaiwa ga gano mutum.
Za mu iya cire ƙunshiya da aka ƙirƙira don gano ƙanana mai zaman kansa idan akwai haɗari ga lafiyar ƙarami, lokacin da Doka ta nema, Gwamnati, Amintaccen Aboki, ko ƙarami ne ko iyayen ƙanana / shari'a suka ba da rahoton ƙunshiyar kanta. waliyyi
Ƙwarewar mai amfani da kaya
Duba wasu misalai na yadda ɗabbaƙa doka take ga mutanen da suke kan Facebook, kamar: yadda zai kasance wajen kai rahoton abin da kake ganin bai kamata ya kasance a Facebook ba, a faɗa maka cewa ka karya dokar Tsarin Rayuwar Al'ummarmu da kuma ganin allon gargaɗi a kan wani bayani.
Lura: A kullum muna ƙara ingantawa, saboda haka ta yiwu abin da ka gani a nan tsoho ne idan aka kwatanta shi da abin da muke amfani da shi a yanzu.
KWAREWAR MAI AMFANI
Kai rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Sadarwa bayan rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Kwarewar sauke abu
KWAREWAR MAI AMFANI
Allunan gargaɗi
Bayanai
Duba sabon bayani game da Rahoton Tilasta Bin Tsarin Rayuwar Al'umma
Ɗabbaƙa doka
Muna da manufofi iri ɗaya a duk faɗin duniya, ga duk waɗanda ke kan Facebook.
Ma’aikata da ke sake dubawa
Ƙungiyarmu ta duniya da ke ɗauke da masu bita sama da 15,000 suna aiki kowace rana don kare lafiyar mutane a Facebook.
Aiki tare da masu ruwa da tsaki
Ƙwararru daga waje, malamai, ƙungoyoyin da ba na gwamnati ba da masu tsara dokoki suna taimakawa wajen samar da Tsarin Al'ummar Facebook.
Sami taimako a kan ci da gumin yara ta hanyar lalata da cin zarafi da nuna tsiraici
Sami bayani a kan abin da za ka iya yi idan ka ga wani abu a Facebook da ya saɓa wa Tsarin Al'ummarmu.
Ziyarci Cibiyar Taimakonmu