Cin zali da Kyara
Cikakken bayanin doka
CANZA SHIGA
Yau
23 Jan, 2025
3 Yul, 2024
14 Dis, 2023
29 Sat, 2023
30 Yun, 2023
31 Mar, 2023
27 Jan, 2023
30 Sat, 2022
24 Dis, 2021
14 Okt, 2021
27 Agu, 2021
5 May, 2021
3 Afrilu, 2021
29 Jan, 2021
19 Nuw, 2020
31 Yul, 2020
29 May, 2020
28 Fab, 2020
31 Jan, 2020
17 Dis, 2019
30 Sat, 2019
31 Yul, 2019
2 Yul, 2019
27 Afrilu, 2019
Ra'ayin Doka
Cin zali da matsantawa kan faru a wurare da dama kuma suna zuwa a sigogi daban-daban daga yin barazana da sakin bayanan gano mutum zuwa aika saƙonnin barazana da kuma yin tuntuɓa ta mugunta wadda ba a so ba. Ba ma ƙyale irin wannan ɗabi’a saboda tana hana mutane jin suna da kariya da samun girmama su a kan Facebook, nstagram da Threads.
Mukan rarrabe tsakanin fitattun mutane da kuma ɗaiɗaikunsu saboda muna son bayar da damar tattaunawa, wanda yawanci yakan haɗa da sharhi na-suka ga mutanen da suka fito a labarai ko waɗanda suke da yawan masu kallonsu. Ga fitattun mutane, mukan cire sukar da suke da tsanani tare da wasu nau’o’in sukar inda ake maƙala fitaccen mutumin kai tsaye a cikin wallafa ko jawabi. Muna fassara fitattun mutane a matsayin jami’an gwamnati a matakin jiha da ƙasa, ‘yan takarar siyasa da ke neman waɗannan muƙaman, mutane da ke da masoya ko mabiya sama da miliyan ɗaya a kafafen sada zumunta da kuma mutanen da ke fitowa sosai a labarai.
Ga ɗaiɗaikun mutane, kariyarmu tana wuce haka: Mukan cire bayanai waɗanda aka yi nufin wulaƙantarwa ko kunyatarwa, da suka haɗa da ga misali, iƙirari game da al’amuran jima’i da ya keɓanci wani. Mun yarda cewa takurawa da matsantawa za su fi yin tasiri a ƙwaƙwalen yara, wanda hakan ne ya sa manufofinmu suke bayar da tsananin kariya ga kowa wanda ya kai shekaru 18, ba tare da la’akari da matsayin mai amfani ba.
Muhalli da niyya su ne abin dubawa, inda mu kan ba da dama ga mutane su yi wallafa tare da yaɗawa idan muka lura cewa an yaɗa wani abu domin a kushe a jawo hankali ga al’amarin takurawa da matsantawa. A wasu al’amuran, mukan buƙaci samu rahoto da kai saboda yana taimaka mana mu fahimci cewa mutumin da ake yi wa ya damu da takurawa da kuma matsantawar. Baya ga kawo rahoton irin wannan ɗabi’a da bayani, mukan ƙarfafi mutane su yi amfani da kayan aiki da ake da su a dandalinmudon taimakawa a bayar da kariya daga hakan.
Haka kuma muna da Cibiyar Hana Zalunci, wadda wurin samun bayanai ne ga matasa, iyaye, da masu koyarwa da suke neman taimako kan al’amura masu alaƙa da zalunci da sauwran rikice-rikice. Tana bayar da bayanan jagoranci daki-daki da suka haɗa da bayani kan yadda za a fara muhimmiyar hira kan zalunci. Sami ƙarin bayani kan abin da muke yi don kare mutane daga zalunci da matsantawa a nan.
Lura: Wannan doka ba ta shafi ɗaiɗaikun mutanen da suke cikin ƙungiyoyin da aka ayyana a ƙarƙashin dokar Ƙungiyoyi Masu Hatsari da ɗaiɗaikun mutane bako ɗaiɗaikun mutanen da suka mutu kafin 1900.
Mataki na 1: Kariyar bai-ɗaya ga kowa da kowa:
- Kowa da kowa na samun kariya daga:
- Adireshin da ba a da buƙata da su:
- An maimaita, KO
- Cin zarafi ta jima’i, KO
- Ab nufa kan taron mutane masu yawa ba tare da an roƙi yin hakan ba.
- Kiraye-kiraye don aikata yi wa kai-rauni ko kashe kai na wani mutum a keɓe ko rukunin mutane.
- Cin zarafi a matsayin waɗanda aka yi wa fyaɗe, cin zarafin jima’i, tsangwamar neman yin jima'i, ko cin zarafi na gida.
- Jawaban bayyana niyyar aikata jima’i ko neman su shiga cikin aikata yin jima’i.
- Yin sharhi mai ɗauke da tsauraran kalmomin jima’i.
- Izgilancin haɗa hoton jima’i ko zane-zane
- Cin zarafin ta hanyar kalmomin musgunawa masu alaƙa da yin jima’i (misali: karuwa, matar banza).
- Iƙrarin cewa wani mummunan al’amarin musgunawa bai faru ba.
- Iƙrarin cewa ɗaiɗaikun mutane suna ƙarya game da kasancewarsu waɗanda al’amarin tashin hankali ko harin ‘yan ta’adda ya shafa, da suka haɗa da iƙrarin cewa suna:
- Kwatantawa ko ƙaryar kasancewa wanda wani keɓaɓɓen abu ya shafa, ko
- Wanda aka biya ko aka ɗauka don ruɗar mutane game da rawar da suka taka a sha’anin.
- Barazanar sakin lambar wayar ɗaiɗaikun mutane, adireshin wurin zama, adireshin imel ko bayanan lafiya (kamar yadda aka bayyana a Dokar Keta Sirri).
- Kiraye-kiraye ga ko yin jawaban bayyana niyya domin aikatawa, cin zali da/ko cusgunawa.
- Bayanin da ke ƙara ƙasƙantar da ko bayyana ƙyama ga ɗaiɗaikun mutanen da aka nuna yayin da suke yin, ko bayan ƙare, jinin al’ada, fitsari, amai, ko kashi
- Ana bai wa kowa kariya daga waɗannan, amma ga sanannun mutane na al’umma, dole ne bisa niyya su fuskanci:
- Kiraye-kirayen mutuwa da kuma jawaban da ke goyon bayan ɗauka ko samun wani hali na rashin lafiya.
- Yin murna ko aibata mutuwa ko halin rashin lafiya.
- Iƙrari game da cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima’i.
- Jawaban ƙasƙanci game da siffar jiki.
Mataki na 2: Ƙarin kariya ga dukkan Yara, Keɓaɓɓun Manya da Fitattun Mutane Masu Taƙaitaccen Matsayi (misali, mutanen da tushen shaharar su ya taƙaita ga gwagwarmayarsu, aikin jarida, ko waɗanda suka shahara ta hanyoyin da ba yin su ba ne) tare da:
- Ƙari akan kariyar bai-ɗaya ga kowa da koa, dukkan yara (ɗaiɗaikun mutane da sanannun mutane), keɓaɓɓun manya da sanannun mutane masu taƙaitaccen matsayi suna samun kariya daga:
- Iƙrari game da yin jima’i ban da a yanayi na zargin aikata laifuka a kan manya (taɓa jiki da niyyar jima’i ba bisa yarda ba).
- Bayanin da ke yin jima’i da wani babba (yin jima’i da yara yana cikin dokar Ci Da Gumin Yara ta Hanyar Jima’i, Cin Zarafi da Tsiraici).
- Dukkan yara (ɗaiɗaikun mutane da sanannun mutane), keɓaɓɓun manya da sanannun mutane masu taƙaitaccen matsayi suna samun kariya daga waɗannan, amma ga sanannun yara na al’umma, dole ne bisa niyya su fuskanci:
- Kwwatancin wulaƙantarwa (a rubuce ko a hoto) ga ko game da:
- Dabbobi da ƙwari, da suka haɗa halittu masu kama da mutum, waɗanda a al’adance ake ganin su ƙasƙantattu.
- Bakteriya, ƙwayoyin cuta, ƙwayoyin halitta da cututtuka.
- Abubuwa marasa rai da suka haɗa da bola, ƙazanta, kashi.
- Bayanin da aka yi amfani da shi don haskaka, da’ira, ko kuma a jawo hankali ta fuska marar kyau ga wasu keɓaɓɓun siffofi na zahiri (hanci, kunne da sauransu).
- Bayanin da ke ba su matsayi bisa ga siffar jiki ko ɗabi’un halayya.
- Bayanin da ke ƙasƙantar da ɗaiɗaikun mutanen da aka nuna ana cin zalinsu a zahiri (ban da a yanayi na wasan-faɗa).
Mataki na 3: Ƙarin kariya ga Keɓaɓɓun Yara, Keɓaɓɓun Manya, da Sanannun Yara da Ba Na Sa-kai ba:
- Ƙari ga dukkan kariyar da aka lissafa a sama, dukkan keɓaɓɓun yara, keɓaɓɓun manya (waɗanda dole su kai rahoto da kan su), da kuma sanannun yara ba na sa-kai ba suna samun kariya daga:
- Tsinuwar da aka nufa.
- Iƙirari game da hulɗar soyayya, zaɓin abokin jima’i ko shaidar jinsi.
- Kiran a aikata, bayanan niyya, na buri ko jawabai masu sharaɗi, ko jawabai masu nema ko goyon bayan wariya.
- Mummunar ɗabi’a ko iƙirarin iyawa, ban da a yanayi na zargin aikata laifuka da kuma nazarin kasuwanci a kan manya.
- Bayyana jin haushi, ƙyama, ko bayanin da ke ƙin yarda da kasancewar wani mutum, ban da a yanayi na zargin aikata laifi akan manya mutane.
- Yayin da aka kai rahoto da kai, keɓaɓɓun yara, keɓaɓɓun manya, da sanannun yara ba na sa-kai ba daga waɗannan:
- Cin zalin murya na mutum-na-farko.
- Hoton da aka jirkita wanda ba a so.
- Kwatanci da wasu ɗaiɗaikun mutane na almara ko keɓaɓɓun mutane a bisa ga siffar jiki.
- Iƙrari game da shaidar addini ko yin saɓo.
- Kwatanci da dabbobi ko ƙwari waɗanda a al’ada ake ganin su masu naƙasar ƙwaƙwalwa ko ƙasƙantar halitta (“damisa,” “zaki”).
- Bayanan kushe kamanni na tsaka-tsaki ko masu kyau.
- Ɗabi’ar da ba mummuna ba ko iƙrarin iyawa.
- Cin zarafi ta cikin kalmomin izgili masu alaƙa da rashin yin jima’i.
Mataki na 4: Ƙarin kariya ga Keɓaɓɓun Yara kaɗai:
- Yara suna samun mafi yawan kariya ƙarƙashin manufarmu. Ƙari ga dukkan kariyar da aka lissafa a sama, haka kuma ana bai wa keɓaɓɓun yara kariya daga:
- Zarge-zarge game da halayyar aikata laifi ko ta saɓawa doka.
- Bidiyo na cin zali na zahiri a kan ƙananan yara da aka yaɗa a yanayi na yin suka.
- Kalaman izgili masu alaƙa da tsinuwar jinsin mata.
Cin zali da tsangwama ta cikin shafuka, rukunoni, sha’anoni da saƙonni
- Kariyar Matakai na 1 zuwa na 4 suma ana aiwatar da su akan shafuka, rukunoni, sha’anoni da saƙonni.
Don waɗannan Tsarin Rayuwar Al'umma, muna buƙatar ƙarin bayani da/ko a muhallin da za a tilasta:
Ka da ka yi:
- Wallafa bayanin da ke nufar ɗaiɗaikun mutane ta cikin Shafuka, Rukunoni da Sha’anonin da ba a so. Mu kan cire wannan bayani yayin da wanda aka nufa ko wani wakilin da aka ba izini na wanda aka nufa ya kawo rahoton sa.
- Ƙunshiyar da aka wallafa da aka bayyana a sama wanda in ba haka ba zai buƙaci maƙasudi don ba da rahoton ƙunshiyar ko kuma inda ƙunshiyar ya nuna cewa fasta ana nufin wani kai tsaye (misali: an sanya maƙasudin a cikin wallafar ko sharhi). Za mu cire bayanin idan muka sami tabbaci daga wanda aka cutar ko wani wakilin da aka ba izini na wanda aka cutar cewa ba a son bayanin (a raye ko a mace) cewa ba a son wannan ƙunshiyar..
- Wallafa bayanin da ke yin kiran a ko bayyana niyya ta aiwatar da halayyar da za ta kasance cin zali da cusgunawa a ƙarƙashin manufofinmu. Za mu cire wannan bayanin yayin da muka sami tabbaci daga wanda ake nufi ko wakilin da aka ba izini na wanda ake nufi cewa ba a son bayanin.
- Wallafa bayanin da ke mayar da wani fitaccen mutum abin jima’i. Za mu cire wannan bayanin yayin da muka sami tabbaci daga wanda ake nufi ko wakilin da aka ba izini na wanda ake nufi cewa ba a son bayanin.
- Fara tuntuɓar da ke yin lalata da mai karɓa. Za mu cire duk wata ƙunshiya da aka raba a cikin yanayin da ba'a so lokacin da muka sami tabbaci daga mai karɓa, ko wakilin mai karɓa mai izini wanda ba a so.
- Cire cusgunawar mutane da yawa da aka nufa, yayin da:
- Nufar ɗaiɗaikun mutanen da suke tattare da matsananciyar barazanar cutarwa ba a kan intanet ba, ta cikin kowane sarari, da aka fassara da:
- Masu kare haƙƙin ɗan adam
- Ƙananan yara
- Waɗanda Sha’ani/bala’i na tashin hankali ya shafa
- Fitattun ‘yan adawa a cikin ƙasashen da ke cikin barazana a lokutan zaɓe
- Jami’an zaɓe
- Masu adawa da gwamnati waɗanda aka nufa bisa ga matsayin su na masu yin adawa.
- Tsirarun ƙabilu da na addini a yankunan da ake rikici
- Mutumin da ya fito daga rukunin da ke cikin barazana wanda aka ayyana kuma ake ganewa
- Nufar duk wani mutum ta cikin sarari na ƙashin kai, kamar akwatin saƙonni ko furofayil, tare da:
- Bayanin da ke saɓawa manufofin cin zali da cusgunawa ga ɗaiɗaikun mutane ko,
- Bayanin da ake ƙyama da yake bisa wata siffar da aka kare
- Tsayar da asusun da suke aikata cusgunawar mutane da yawa a matsayin ɓangare na ko dai
- Ƙungiyoyin gwamnati ko masu dangantaka da gwamnati da suke nufar duk wani mutum ta cikin kowane sarari.
- Ƙungiyoyin gaba da suke nufar duk wani mutum ta cikin kowane sarari tare da:
- Bayanin da ke saɓawa manufofin cin zali da cusgunawa ga ɗaiɗaikun mutane ko,
- Bayanin da yake nufar su bisa wata siffar da aka kare, ko,
- Bayani ko halayyar da ake ganin abar ƙyama ce a yanayi na yankin
Ƙwarewar mai amfani da kaya
Duba wasu misalai na yadda ɗabbaƙa doka take ga mutanen da suke kan Facebook, kamar: yadda zai kasance wajen kai rahoton abin da kake ganin bai kamata ya kasance a Facebook ba, a faɗa maka cewa ka karya dokar Tsarin Rayuwar Al'ummarmu da kuma ganin allon gargaɗi a kan wani bayani.
Lura: A kullum muna ƙara ingantawa, saboda haka ta yiwu abin da ka gani a nan tsoho ne idan aka kwatanta shi da abin da muke amfani da shi a yanzu.
KWAREWAR MAI AMFANI
Kai rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Sadarwa bayan rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Kwarewar sauke abu
KWAREWAR MAI AMFANI
Allunan gargaɗi
Bayanai
Duba sabon bayani game da Rahoton Tilasta Bin Tsarin Rayuwar Al'umma
Ɗabbaƙa doka
Muna da manufofi iri ɗaya a duk faɗin duniya, ga duk waɗanda ke kan Facebook.
Ma’aikata da ke sake dubawa
Ƙungiyarmu ta duniya da ke ɗauke da masu bita sama da 15,000 suna aiki kowace rana don kare lafiyar mutane a Facebook.
Aiki tare da masu ruwa da tsaki
Ƙwararru daga waje, malamai, ƙungoyoyin da ba na gwamnati ba da masu tsara dokoki suna taimakawa wajen samar da Tsarin Al'ummar Facebook.
Sami taimako a kan Cin zali da Kyara
Sami bayani a kan abin da za ka iya yi idan ka ga wani abu a Facebook da ya saɓa wa Tsarin Al'ummarmu.
Ziyarci Cibiyar Taimakonmu