Nuna Tsiraicin Babba da Saduwar Jima’i

Cikakken bayanin doka

CANZA SHIGA
Ra'ayin Doka
Muna taƙaice nuna tsiraici ko ayyukan jima'i saboda wasu mutane a cikin al'ummarmu na iya damuwa da irin wannan nau'in abin, musamman saboda asalin al'adun nasu ko shekaru.
Mun fahimci cewa za a iya yaɗa tsiraici bisa wasu mabambantan dalilai, da suka haɗa da a matsayin nuna rashin amincewa, domin wayar da kai game da wata manufa, ko domin dalilan ilmantarwa ko na kiwon lafiya. A inda ya dace kuma wannan manufa take a bayyane, mukan ba da dama ga bayanin. Alal misali, yayin da muke ƙayyade wasu hotunan nonon mata da ke nuna kan nono, muna yarda da wasu hotunan, haɗi da waɗanda ke nuna zanga-zanga, mata da ke shayarwa da hotunan taɓon da aka yi wa tiyatar cire nono (wani lokaci ana sanya musu alamar allon gargaɗi na sirri da taƙaicewa bisa ga shekaru). Muna kuma yarda da zane-zane na gaske da ke nuna tsiraici kamar hotunan zane-zane, gumaka, da sauransu (wani lokaci ana yi musu laƙabi da allon gargaɗi na abun sirri da taƙaicewa bisa shekaru). Mukan koma cire hotunan jima’i domin hana yaɗa bayanan da ba babu amincewa ko na masu ƙarancin shekaru.
A ƙarƙashin wannan dokar, muna cire ainihin hotuna da bidiyon tsiraici da ayyukan jima'i, hotunan tsiraici da ayyukan jima'i da aka ƙirƙira ta AI ko kwamfuta, da hotunan dijital, ba tare da la'akari da ko sun yi kama da "ainihi" ba (kamar, mai kama da mutum na gaske). Kamar yadda aka ambata a sama, muna kuma yin la'aƙari da kyau da zane-zane na duniya na ainihi da wasu abubuwan likitanci, ilimi, da wayar da kan jama'a, kuma an fayyace waɗannan a cikin dokar.
An fayyace bayanin da ke da alaƙa da tsiraicin yara a cikin Tsarin Mu’amalar Al'umma ɗinmu Ci Da Gumin Yara ta Hanyar Jima’i da Cin Zarafi da Nuna Tsiraici.
Ba mu yarda da waɗannan abubuwa ga dukkan masu amfani ba:
Tsiraicin Manya
  • Hotuna masu kama da na gaske ko na dijital na tsiraicin manya, idan sun nuna:
    • Al'aura da ake gani (har da lokacin da aka rufe ta da gashin mara ko abubuwan da aka ɗora a kai na naʼura)
    • Dubura da ake gani da/ko hotunan kusa na duwaiwai da ake gani
    • Kan nonon mace da ake gani, sai dai a yanayin shayarwa, ko yanayin yin zanga-zanga
  • Bidiyoyin dijital/masu kama da na gaske da ke mai da hankali kan cinya, nonuwan mata, ko duwawu waɗanda aka ɗauka ba tare da sanin mutum ko mutanen da aka nuna a ciki ba.
  • Lura cewa tare da wasu taƙaicewa, za mu iya yarda da hotunan tsiraicin manya a wasu ƙarin yanayi na musamman, kamar yanayin likitanci ko na lafiya. An bayyana wannan dalla-dalla a sassan da ke ƙasa.
Ayyukan Jima'i Na Manya
  • Hotuna masu kama da na gaske ko na dijital na ayyukan jima'in manya, har da:
    • Yin jima’i a bayyane da kuma motsa sha’awar al’aura:
      • Saduwar jima'i a bayyane ko jima'i ta baki, kamar yadda aka nuna ta bakin mutum ko al'aura suna shiga ko hulɗa da al'aurar wani mutum ko dubura, ko kuma al'aurar da aka sanya a kan ko aka saka a cikin abun wasan jima'i, lokacin da aƙalla al'aurar mutum ɗaya ko dubura ta bayyana
      • Motsa sha’awar al’aura ko dubura a bayyane, kamar yadda aka nuna ta motsa sha’awa, ko shigar da kayan wasan jima’i cikin al’aura ko duburar mutum, yayin da ake ganin haɗuwar al’aura ko dubura kai tsaye
    • Ayyukan jima'i ko tayar da sha'awa a ɓoye:
      • Saduwar jima’i a bayyane ko jima’i na baki, kamar yadda aka nuna da shigar da baki ko al’aura ko taɓa al’aura ko duburar wani mutum, yayin da al’aura ko duburar da/ko shigar ko taɓawar ba a ganinta kai tsaye.
      • Motsa al'aura ko duburar mutum a ɓoye, wanda ke bayyana ta hanyar motsawar kanta, ko sanya kayan wasan jima'i a kan al'aura ko dubura ko kuma cikinsu, ko kuma al'aura da aka sanya a kan kayan wasan jima'i ko aka shigar da ita cikinsa, a lokacin da ba a iya ganin al'aurar ko duburar, motsawar, sanyawar, ko shigarwar kai tsaye ba.
      • Ayyukan jima'i da ke gab da faruwa, kamar tsayuwar da ke nuna cewa muʼamala na gab da farawa tsakanin hannun mutum, baki ko al'aura da al'aurar wani mutum ko dubura ta nuna.
    • Wasu ayyukan jima'i ko tayar da sha'awa:
      • Miƙewar mazakuta
      • Bayyanar abubuwan da ake samu bayan yin jima’i
      • Kayan wasan jima’i da aka ɗora a saman baki ko aka shigar ciki
      • Motsa sha’awar nonuwan mutum da ake gani
      • Matsar nonon mace, da aka fassara da motsin damƙa da yatsu a tanƙwashe da ke nuna duka zane da fitar sauyin surar nonon. Mukan ba da damar matsa a yanayin shayar da nono.
    • Hoto mai kama da na gaske ko na na'ura ko zane na zahiri wanda ke nuna matsananciyar sha'awa ta musamman wanda ya haɗa da waɗannan:
      • Ayyukan da za su iya kai wa ga mutuwar mutum ko dabba
      • Yanke sassan jiki
      • Cin naman mutum
      • Kashi, fitsari, tofi, majina, jinin al’ada ko amai
      • Dabbanci
      • Jima’in makusanta
      • BDSM (ɗauri da horo, mallaka da biyayya, jin daɗin azabtarwa da jin daɗin karɓar azaba), sai dai idan alamun jima'i suma suna nan
  • Hotunan da suka yi kama da na gaske na ayyukan jima'i a fili ko tada sha'awa a yanayin likitanci ko na lafiya
  • Sautin murya na saduwar jima’i da aka tsawaita
  • Lura cewa tare da wasu taƙaicewa, za mu iya yarda da hotunan ayyukan jima'i a yanayi na musamman, kamar yanayin likitanci ko na lafiya. An bayyana wannan dalla-dalla a sassan da ke ƙasa.
Ga waɗannan abubuwa, muna iyakance damar duba abun ga masu amfani, masu shekaru 18 da sama da haka kuma mun haɗa da laƙabi domin mutane su san cewa abun na iya zama na sirri:
  • Hotunan naʼura da zanen zahiri na ayyukan jima'i ko tayar da sha'awa a bayyane a yanayin likitanci ko na lafiya
  • Hotuna masu kama da na gaske ko na naʼura da zane na zahiri na ayyukan jima'i ko tayar da sha'awa a ɓoye ko wasu a yanayin likitanci ko na lafiya
  • Hotunan da suka yi kama da na gaske/na dijital da zanen zahiri na al'aurar da ake iya gani, duburar da ake iya gani, hotunan da aka ɗauka kusa na mazaunan da ake iya gani ko kan nonon mata da ake iya gani a yanayin tiyatar tabbatar da jinsi
  • Zanen zahiri na al'aura da ake gani (har da al'aurar da aka rufe ta da abubuwan da aka ɗora a kai na naʼura ko aka rufe da gashin mara kaɗai), dubura da ake gani, hotunan kusa na duwaiwai da ake gani ko kan nonon mace da ake gani, inda tsiraicin shi ne abin da hoton ya fi mayar da hankali a kai kuma ba a yanayin likitanci ko na lafiya ba
  • Hotuna masu kama da na gaske ko na naʼura na al'aura da ake gani (har da al'aurar da aka rufe ta da abubuwan da aka ɗora a kai na naʼura ko aka rufe da gashin mara), hotunan kusa na duwaiwai da ake gani, dubura da ake gani ko kan nonon mace da ake gani, lokacin da aka raba a yanayin yunwa, kisan ƙare dangi, laifukan yaƙi, ko laifukan cin zarafin bil'adama
Ga bayanai masu zuwa, mukan taƙaita damar ganin bayanin ga manya, ‘yan shekaru 18 zuwa sama;
  • Hotuna masu kama da na gaske/na naʼura da ke nuna mutum kusan tsirara kamar tsiraicin da aka rufe shi kawai ta hanyar abubuwan da aka ɗora a kai na naʼura ko abu marar haske da wasu lokuta na tsiraicin da aka rufe ta tufafi masu haske
  • Hotutuna masu kama da na gaske/na naʼura da ke nuna mutane inda gaba, duwaiwai ko ƙirjin mace su ne abin da hoton ya fi mayar da hankali a kai
  • Hotuna masu kama da na gaske ko na naʼura da zanen zahiri na ayyukan jima'i ko tayar da sha'awa a bayyane, a ɓoye ko wasu lokacin da siffofin jiki ko kwane-kwane kawai ake gani
  • Zane na duniyar gaske, inda
    • Hotuna masu nuna ayyukan jima'i ko tayar da sha'awa a ɓoye, a bayyane, ko wasu sai dai idan an aika a yanayin likitanci ko na lafiya
    • Hoton da ke nuna dabbanci, matuƙar an yaɗa shi tsaka-tsaki ko don yin alla-wadai sannan kuma mutane ko dabbobin da aka nuna ba na gaske ba ne.
  • Gane hotuna masu kama da na gaske na almara waɗanda ke nuna ayyukan jima'i ko tayar da sha'awa a ɓoye ko wasu
  • Hotuna masu kama da na gaske ko na dijital da zane na zahiri da ke nuna:
    • Ayyukan da suka shafi jima'i kamar sumbata da harshe da ake gani da rawa ta jima'i ko ta tayar da sha'awa
    • Mutane da ke kwaikwayon ayyukan jima'i
    • Alamu da ke nuna al'aura, wasa da al'aura, jima'i ta baki, ko saduwa ta jima'i
    • Alamomin kamfani, hotunan allon sikirin ko gajerun bidiyoyi na sanannun shafukan yanar gizo na batsa
  • Abun ciki da ke ɗauke da sautin ayyukan jima'i
Ga waɗannan abubuwan, mun haɗa da wata alama domin mutane su san cewa bayanin zai iya kasancewa na taka-tsantsam:
  • Hotuna masu kama da na gaske/ na dijital da zane na zahiri da ke nuna:
    • Al'aura da ake gani (haɗi da al'aurar da aka rufe ta da abubuwan da aka ɗora a kai na naʼura ko aka rufe da al'aurar da aka rufe ta da gashin mara), hotunan kusa na duwaiwai da ake gani, ko dubura, idan an yaɗa a muhalli na likitanci ko na lafiya. Wannan zai iya haɗa wa da, alal misali:
      • Halaye na haihuwa da bayan haihuwa
      • Binciken-kai don gano cutar sankara ko sauran cututtuka
  • Kan nonon mace da ake gani, lokacin da aka raba a yanayin likitanci ko na lafiya (har da cire nono ko aiki a kan wanda ya tsira daga cutar ciwon daji)
Don waɗannan Tsarin Rayuwar Al'umma, muna buƙatar ƙarin bayani da/ko a muhallin da za a tilasta:
  • A wasu lokutan, za mu yarda da abu ga masu shekaru 18 zuwa sama tare da laƙabi wanda ƙila zai iya karya Tsarin Rayuwar Al'umma idan an tabbatar da cewa abun na ba'a ne. Za a ba da izinin bayani ne kawai idan abubuwan da suka saɓa bayani ana juyar da su zuwa ba’a ne ko danganta su da wani abu ko wani mutum daban domin yi musu ba'a ko suka su.
Ƙwarewar mai amfani da kaya
Duba wasu misalai na yadda ɗabbaƙa doka take ga mutanen da suke kan Facebook, kamar: yadda zai kasance wajen kai rahoton abin da kake ganin bai kamata ya kasance a Facebook ba, a faɗa maka cewa ka karya dokar Tsarin Rayuwar Al'ummarmu da kuma ganin allon gargaɗi a kan wani bayani.
Lura: A kullum muna ƙara ingantawa, saboda haka ta yiwu abin da ka gani a nan tsoho ne idan aka kwatanta shi da abin da muke amfani da shi a yanzu.
KWAREWAR MAI AMFANI
Kai rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Sadarwa bayan rahoto
KWAREWAR MAI AMFANI
Kwarewar sauke abu
KWAREWAR MAI AMFANI
Allunan gargaɗi
Bayanai
Duba sabon bayani game da Rahoton Tilasta Bin Tsarin Rayuwar Al'umma
Ɗabbaƙa doka
Muna da manufofi iri ɗaya a duk faɗin duniya, ga duk waɗanda ke kan Facebook.
Ma’aikata da ke sake dubawa
Ƙungiyarmu ta duniya da ke ɗauke da masu bita sama da 15,000 suna aiki kowace rana don kare lafiyar mutane a Facebook.
Aiki tare da masu ruwa da tsaki
Ƙwararru daga waje, malamai, ƙungoyoyin da ba na gwamnati ba da masu tsara dokoki suna taimakawa wajen samar da Tsarin Al'ummar Facebook.
Sami taimako a kan nuna tsiraicin babba da lalata
Sami bayani a kan abin da za ka iya yi idan ka ga wani abu a Facebook da ya saɓa wa Tsarin Al'ummarmu.
Ziyarci Cibiyar Taimakonmu