Tsarin Rayuwar Al'umma

Tsarin Rayuwar Al'umma ya bayyana abin da aka yarda da wanda ba a yarda ba a Facebook, Instagram, Messenger da Threads.
Gabatarwa
An samar da waɗannan tsayayyun ma’aunin ne daga martanin da mutane suke yi da kuma shawarar ƙwararru a fagen fasaha da tsaron al’umma da haƙƙoƙin ɗan’adam. Domin tabbatar da cewa ana ƙimanta ra’ayin kowa, mukan ba da matuƙar kulawa don samar da tsayayyun ma’aunin da suka ƙunshi mabambantan ra’ayoyi da aƙidoji, musamman na mutane da al’ummomin da wataƙila aka ware ko aka danne su.
A kowace rana, mutane suna amfani da Facebook, Instagram, Messenger da Threads don raba abubuwan da suka fuskanta, haɗuwa da abokai da iyali, da kuma gina al'umma. Ayyukanmu suna ba biliyoyin mutane damar bayyana kansu a cikin ƙasashe da al'adu daban-daban da kuma harsuna da dama.
Meta ya fahimci yadda ake ganin muhimmancin Facebook, Instagram, Messenger da Threads a inda mutane ke jin ƙarfin yin magana, kuma muna ɗaukar nauyinmu da muhimmanci wajen kawar da cin zarafi daga aikin. Wannan shi ne dalilin da ya sa muka samar da tsare-tsare don abin da aka yarda da wanda ba a yarda ba a kan waɗannan ayyukan.
A lura da cewa samfurin tsarin Rayuwar Al'umma da ke cikin Ingilishin Amurka ya ƙunshi yawancin dokokin da aka sabunta kuma shi ya kamata a yi amfani da shi a matsayin bayanai na farko.
Jajircewarmu ga bayar da damar yin magana
Manufar Tsarin Mu’amalar Al'ummarmu ita ce a samar da wani wuri na bayyana ra’ayi da bai wa mutane damar yin magana. Meta yana son mutane su iya yin magana a fili a kan al’amuran da suka dame su, ko da kuwa wasu za su ƙi yarda ko za su gan su a matsayin abin a yi watsi da su ne. A wasu lokutan, mukan bar bayanai —da suka saɓa wa tsarinmu dama —idan sun isa zama labari kuma hakan ya kasance shi ne masalahar al’umma. Mukan yi hakan ne kaɗai bayan la’akari da yawan masalahar a kan haɗarin cutarwa sannan mukan kalli tanade-tanaden haƙƙoƙin ɗan’adam na duniya a wajen zartar da wannan hukuncin. A wani yanayin, mukan iya cire bayanai da suke ɗauke da zantuka masu harshen damo ko masu kaikaitattu wanda wani hali kan sa mu fahimci cewa waɗannan bayanai sun saɓa wa tsare-tsarenmu.
Jajircewarmu ga damar bayyana ra’ayi ita ce kan gaba, amma mun yarda cewa kullum intanet yana samar da sababbin damammaki na cin zarafi. Saboda waɗannan dalilai, yayin da muka taƙaita damar bayyana ra’ayi, muna yin hakan ne bisa aiki da ɗaya ko fiye daga cikin waɗannan ɗabi’u:
SAHIHANCI
Muna son mu tabbatar da cewa abubuwan da mutane ke gani suna da sahihanci. Mun yi imanin cewa sahihanci na ƙirƙirar yanayi mafi dacewa don rabawa, kuma wannan ne ya sa ba ma son mutane su yi amfani da ayyukanmu don ɓata sunan wanda suke ko abin da suke yi.
KARIYA
Mun ƙuduri mayar da Facebook, Instagram, Messenger da Threads wurare masu aminci. Muna cire bayanan da za su iya ba da gudummawa wajen haɗarin cutarwa ga tsaron mutane na zahiri. Ba a amincewa da abubuwan da ke yin barazana ga mutane wanda ka iya tsoratarwa ko ware wasu ko hana wasu magana a kan ayyukanmu.
SIRRI
Mun ƙuduri aniyar kare sirri da bayanai na ƙashin kai. Sirri yana ba mutane ‘yancin su bayyana haƙiƙanin yadda suke, su kuma zaɓi yadda da kuma lokacin da za su yaɗa bayanai a ayyukanmu da kuma haɗuwa da mutane cikin sauƙi.
MUTUNCI
Mun yarda dukkan mutane daidai suke game da mutunci da haƙƙoƙi. Muna tsammanin cewa mutane za su girmama mutuncin wasu kuma ba za su kyara ko wulaƙanta wasu ba.
Tsarin Rayuwar Al'umma
Tsarin Mu’amalar Al'ummarmu sun shafi kowa, a ko’ina a faɗin duniya, da kuma dukkan nau’ikan bayani, da ya haɗa da bayanin da aka smar daga AI.
Kowane sashe na Tsarin Mu’amalar Al'ummarmu yana farawa ne da “Hikimar Manufa” wadda ta ke shimfiɗa muradan manufar biye saɗarorin manufa na musamman da suke bayyana:
Bayanan da ba a yarda da su ba; da kuma
Bayanan da suke buƙatar ƙarin bayani ko yanayin da za a ɗabbaƙa su a kai ko bayanan da aka yarda da su amma tare da allon gargaɗi ko bayanan da aka yarda da su amma manya da suka kai shekara 18 ko suka haura ne kaɗai za su iya gani.