Taimaka wa Matasa Su Ga Abubuwan Da Suka Dace Da Shekarunsu
AN SABUNTA 4 MAY, 2026
Muna son matasa su sami ƙwarewa cikin aminci, mai kyau a Facebook da Instagram, wanda ya haɗa da taimaka musu su bincika abubuwan da suke sha'awa yayin nuna musu abubuwan da suka dace da shekarunsu. Muna aiki don hana matasa ganin abubuwan da ba su dace ba ta hanyoyi uku: cire abubuwa gaba ɗaya lokacin da suka karya dokokinmu, ɓoye wasu nau'ikan abubuwan manya ko na sirri daga matasa, da kuma samun ƙaƙƙarfan matakin abin da muke ba da shawara.
Muna ci gaba da haɓaka hanyoyinmu don taimakawa wajen tabbatar da cewa muna ba matasa ƙwarewa mai aminci da dacewa da shekarunsu, da kuma haɗa mafi kyawun bincike da shawarwari daga ƙwararru don samar da kwanciyar hankali ga iyaye. Haka kuma muna so mu ƙara dacewa da wani tsari mai zaman kansa wanda iyalai suka riga suka saba da shi, don haka mun duba ƙa'idojinmu na dacewar shekaru - ƙa'idojin da ke nuna ƙunshiya da muke ɓoye wa matasa tare da guje wa ba su shawararsa - tare da kwatanta su da kimar fina-finai na masu shekaru 13+ da kuma martanin iyaye. Wannan yana nufin manufarmu ita ce matasa su ga ƙunshiya a Instagram da Facebook wanda ya yi kama da abin da za su gani a cikin fim ɗin da ya dace da shekarunsu, a matsayin na asali.
Kamar dai yadda za ka iya ganin wasu abubuwa masu nuni da jima'i ko jin wasu kakkausan kalamai a cikin fim ɗin da aka kimanta ya dace da shekaru sama da 13, matasa za su iya ganin irin wannan abu lokaci-lokaci a Instagram ko/da Facebook - amma za mu ci gaba da yin duk abin da za mu iya don tabbatar da cewa irin waɗannan lokuta sun kasance ƙalilan yadda zai yiwu. Mun gane cewa babu wani tsari da ya kasance mafi ƙyau, kuma mun himmatu wajen ingantawa a kan lokaci.
Akwai bambance-bambance da yawa tsakanin kafofin sada zumunta da fina-finai. Ba mu yi aiki da MPA ba lokacin da muke sabunta saitunan ƙunshiyarmu, kuma ba sa kimanta wata ƙunshiya a Instagram ko/da Facebook, kuma ba sa goyon baya ko amincewa da saitunan ƙunshiyarmu ta kowace hanya. Maimakon haka, mun yi koyi ne daga jagororin jama'a na MPA, waɗanda iyaye suka riga suka saba da su, da kuma martani daga iyaye. Tsarinmu na kula da ƙunshiya ba ɗaya yake da na hukumar sanya kimar fina-finai ba, don haka yanayin ƙwarewar na iya zama ba iri ɗaya bane gaba ɗaya.
Matakai daban-daban na Kariya
Ga kowa da kowa: Muna cire abubuwan da suka karya Tsarin Rayuwar Al'ummarmu. Muna kuma da babban mataki ga nau'in abubuwan da muke ba da shawara.
❌ Abubuwan da Muke CirewaTsarin Rayuwar Al'ummarmu ya bayyana nau'ikan abubuwan da ba mu yarda da su ba a Facebook da Instagram. Muna cire waɗannan abubuwan gaba ɗaya ga kowa - har da matasa - duk lokacin da muka sani game da su. Idan muka cire abubuwan da suka karya waɗannan dokoki, za mu iya kuma sanya alamar gargaɗi ga asusun da ya raba su, kuma mu kashe asusun da ya ci gaba da karya dokokinmu ko kuma ya karya su ta mummunar hanya. An tsara waɗannan dokoki ne don kare kowa a cikin al'ummarmu, har da matasa.
Nau'in abubuwan da muke cirewa gaba ɗaya sun haɗa da, amma ba'a iyakance ga:
Cin zarafi da Amfani da Mutane
Ba mu yarda da abubuwan da za su iya cin zarafin mutane ko amfani da su ba, kamar sakonnin da ke ƙarfafa ayyukan jima'i ba tare da yarda ba, ko raba ko neman kayan cin zarafin yara. Misali, za mu cire:
❌ Sakon da ke bayar da tayin karuwanci ko roƙon wani ya aika musu da batsa.
❌ Hoton wani a cikin wani yanayi na jima'i, wanda aka raba ba tare da yardarsa ba.
❌ Sakon da ke bayarwa ko roƙon kayan cin zarafin yara ko hotunan yara tsirara.Kashe-kai, yi wa kai rauni, da Cutar cCn Abinci
Ba mu yarda da abubuwan da ke ƙarfafawa, yabawa ko tallata kisan kai, yi wa kai rauni ko rashin cin abinci ba, yayin da har yanzu muna ba mutane dama su yi magana game da abubuwan da suka faru da su da kuma neman taimako. Misali, za mu cire:
❌ Aiken da ke magana mai kyau game da kisan kai, yi wa kai rauni, ko cutar cin abinci.
❌ Labarin da ke nuna hoton yi wa kai rauni.
❌ Jawabin da ke yi wa wani ba'a saboda cutar cin abinci.
Ɗabiʼar Ƙiyayya, Wulaƙantawa da Barazana
Ba mu yarda da abubuwan da za su iya haifar da yanayin tsoro ko warewa ba, gami da wulaƙantawa da barazana Misali, za mu cire:
❌ Aiken da ke amfani da kalaman wulaƙanci ga mutane bisa launin fata, addini, ƙabila, asalin jinsi, ko kuma ɗabi'ar jima'i.
❌ Jawabin da ke yi wa waɗanda aka yi wa fyaɗe ba'a.
❌ Sakon da ke barazanar fitar da bayanan sirri (kamar lambar fasfo) ko kuma tayar da hankali ga wani.
Kayayyaki da Ayyukan Da Aka Taƙaita
Ba mu yarda da saye, sayarwa, ko cinikin wasu kayayyaki da ayyuka da aka taƙaita a dandamalinmu ba. Haka kuma ba ma yarda mutane su tallata wasu nau'ikan abubuwa ko ba da umarni kan yadda ake amfani da su ba. Misali, za mu cire:
❌ Labari da ke ba da tayin saya, sayarwa, ko musayar nau'ikan kwayoyi daban-daban.
❌ Aike da ke neman saya, sayarwa, ko musayar taba, nikotine, ko barasa.
❌ Jawabi da ke ba da sassan bindiga da aka buga ta na'urar 3D.Muna yin wasu banbancen ga halastattun kasuwancin da ke ba da wasu nau'ikan kayayyaki ƙayyadaddu bisa doka.
Barazana da Hoto mai ɗauke da Bayani
Ba ma yarda da abubuwan hoto mai ɗauke da bayani, ko abun ciki da ka iya zama barazana ga tsaron mutum, kamar barazanar tashin hankali ga mutane. Misali, za mu cire:
❌ Aike da ke barazanar kashe ko sace wani mutum, ko wanda ke ƙarfafa wasu su aikata tashin hankali.
❌ Bidiyo mai ɗaukar hankali da ke nuna wani mutum da aka yi wa ɓarna ko kuma ya ƙone sosai.
Muna yin wasu banbancen ga abubuwan hoto mai ɗauke da bayani a cikin yanayin lafiya ko lokacin da aka raba shi don wayar da kan mutane. Inda muka yarda da abun ciki wanda ke da hoto mai ɗauke da bayani, yawanci mukan rufe shi da allon gargaɗi don sanar da mutane cewa abun cikin na iya zama mai tayar da hankali kafin su danna shi.
Tsiraici, Ayyukan Jima'i, da Kalaman Batsa
Mun ƙayyade nuna tsiraici ko ayyukan jima'i da kuma kalaman batsa. Misali, za mu cire:
❌ Hoto ko bidiyo da ke ɗauke da tsiraici ko bayyanannun ayyukan jima'i, haɗi da lokacin da AI ya samar da su.
❌ Labari da ke da bayyanannun ko kwatance masu hoto na haɗuwar jima'i (sai dai idan abin ban dariya ne ko na barkwanci).
Mun fahimci cewa za a iya yaɗa tsiraici bisa wasu mabambantan dalilai, da suka haɗa da a matsayin nuna rashin amincewa, domin wayar da kai game da wata manufa, ko domin dalilan ilmantarwa ko na kiwon lafiya. A inda ya dace kuma wannan manufa take a bayyane, mukan ba da dama ga wannan abun ciki.
Don cikakkun bayanai kan abubuwan da muke cirewa, duba Tsarin Rayuwar Al'ummar mu.
🛡️ Abubuwan Da Muke Gujewa Ba Da Shawara A KansuMuna ba da shawarwari a wurare kamar Reels ko Explore na Instagram ko Feed na Facebook don taimaka wa mutane gano sababbin kunshi da za su iya sha'awa. Muna da jagorori game da irin abun cikin da za a iya bayar da shawararsa, kuma muna gujewa ba da shawarar abubuwan da ba su da inganci, abin ƙyama, ko kuma na sirri—ko da kuwa abun cikin bai yi tsanani ba na a cire shi. Wannan saboda muna ganin ya kamata a sami ƙa'idodi masu tsauri yayin nuna wa mutane abubuwa daga asusun da ba su zaɓa su bi ba.
⚠️ Ƙarin Abubuwan Da Muke Ɓoyewa Daga Matasa
Matasa: Muna ba da ƙarin kariya ga matasa 'yan ƙasa da shekaru 18. Muna ɓoye ƙarin abubuwa, fiye da abin da muke cirewa ga kowa da kowa, kuma muna guje wa ba da shawarar abubuwa ga matasa waɗanda ake iya ba da shawara ga manya. Manufarmu ita ce matasa su ga ƙunshiya a Instagram da Facebook wanda ya yi kama da abin da za su gani a fim ɗin da ya dace da shekarunsu, a matsayin na asali. Matasa za su iya shiga wani saiti na uku, mai sassauci - wanda ake kira Ƙarin Abubuwa - da izinin iyaye. A Instagram, matasa ko iyayensu za su iya zaɓar wani saiti mai tsauri da ake kira Iyakantattun Abubuwa, kuma matasa za su iya shiga wani saiti na uku, mai sassauci - wanda ake kira Ƙarin Abubuwa - da izinin iyaye
13+ (na asali): 13+ (na asali): Saitin ƙunshiya na 13+ ya yi koyi ne daga kimar fina-finai na masu shekaru 13+ da kuma martanin iyaye, kuma a kunne yake ga matasa a matsayin na asali. Mun yi aiki da ƙwararru kan al'amuran matasa a faɗin duniya don ƙara fahimtar irin nau'o'in ƙunshiyar da za su iya dacewa da manya, amma sun yi wa matasa 'yan ƙasa da shekaru 18 girma da yawa, sannan mun duba waɗannan ƙa'idoji na dacewar shekaru tare da kwatanta su da kimar fina-finai na masu shekaru sama da 13 da kuma martanin iyaye. A wannan saitin, za mu ɓoye ƙarin abubuwa daga matasa fiye da abin da muka riga muka cire ga kowa da kowa. Wannan yana nufin, yayin da manya za su ci gaba da samun damar shiga wannan abun ciki, matasa ba za su iya gani ko yin hulɗa da shi ba, koda kuwa wani asusu da suke bi a cikin Sashin-labarai ko Labarai ne ya raba shi. Za mu kuma hana matasa gano, bi da kuma tattaunawa da asusun da galibi ke raba abubuwan da ba su dace da shekaru ba.
Latsa nan don ka ga wasu daga cikin nau'o'in abubuwan da za mu ɓoye wa matasa a wannan saiti na asali
Kashe-kai, yi wa kai rauni, da Cutar Cin abinci
Muna ɓoye wasu abubuwan da suka shafi kisan kai da cutar da kai don kare matasa daga abubuwan da za su iya tayar musu da hankali ko kuma abubuwan sirri. Misali, za mu ƙayyade ga wasu yan shekaru:
⚠️ Aike inda wani ke bayyana ƙwarewarsa ta ƙashin kai game da kisan kai, ji wa kai rauni ko matsalolin cin abinci, sai dai a cikin yanayin murmurewa.
⚠️ Hoto ko bidiyo da ke nuna mutane a asibiti suna kisan mara lafiya idan ba zai warke ba ko taimaka wa kisan kai.
⚠️ Labarin da wani ke magana a kan ɗabi'arsa ta rage kiba da ta wuce gona da iri.
Kayayyaki da Ayyukan Da Aka Taƙaita
Muna ɓoye wa matasa abun ciki wanda zai iya rinjayarsu su shiga cikin ayyukan da ke da haɗari. Misali, za mu ƙayyade ga wasu yan shekaru:
⚠️ Aike da ke tayin sayar da taba, kayayyakin nikotin, barasa, ko bindigogi idan wani halattaccen shagon kasuwanci ne ya raba shi.
⚠️ Wani Labari da ke ƙarfafa mutane su sha ƙwayoyin gudar da hankali (wanda kuma aka sani da entheogens) ko kayayyakin wiwi.
⚠️ Hotuna da ke ɗauke da yadda ake haɗa abubuwan sha masu sa maye.
⚠️ Aiken sayar da kayayyaki ko ayyukan rage kiba.
Barazana da Hoto mai ɗauke da Bayani
Muna ɓoye wa matasa hotuna da bidiyoyi masu ɗaukar hankali da tayar da hankali, koda kuwa mun yarda da shi a bayan allon gargaɗi ga manya. Misali, za mu ƙayyade ga wasu yan shekaru:
⚠️ Hoton mutum da ya ƙone sosai, wanda za mu rufe da allon gargaɗi ga manya.
⚠️ Hoto ko bidiyo na harbe-harbe, zalunci, ko haɗurran mota masu kisa.
Tsiraici, Ayyukan Jima'i, da Kalaman Batsa
Muna ɓoye ƙarin abubuwa daga matasa waɗanda ba su ƙunshi bayyanannen tsiraici ko ayyukan jima'i ba amma za a iya ɗaukar su a matsayin masu nuni da jima'i. Misali, za mu ƙayyade ga wasu yan shekaru:
⚠️ Aiken da ke da kusan tsiraici kamar tsiraicin da aka rufe da wani abu na dijital.
⚠️ Hoton da aka zuƙo a kan ɗuwawun wani.
⚠️ Labari mai ɗauke da kalamai masu nuni da jima'i da ke kwatanta haɗuwar jima'i, haɗi da amfani da karin magana na jima'i.
Don cikakkun bayanai kan abubuwan da muke cirewa, duba Tsarin Rayuwar Al'ummar mu.
Haka nan za mu guji ba da shawarar ƙarin wasu nau'ikan ƙunshiya, ko da kuwa hakan ya dace da kimar fina-finai na masu shekaru 13+ da kuma martanin iyaye. Yawancin abubuwan da muke guje wa ba da shawara ga manya an riga an ɓoye su gaba ɗaya daga matasa, amma ga matasa muna ƙara yin nisa kuma muna guje wa ba da shawarar ƙarin nau'o'in abubuwa - kamar hotuna ko bidiyoyin da za a iya gani a matsayin masu nuni da jima'i a ɓoye, zagi mai ƙarfi, ko kuma wasannin haɗari kamar tsalle daga sama.
Iyakantattun Abubuwa: A Instagram, ga iyayen da suka fi son ƙarin kulawa, mun gabatar da wani sabon saiti mai tsauri sosai wanda ake kira Iyakantattun Abubuwa. Yayin da aka kunna saitin Iyakantattun Abubuwa, za mu yi amfani da matatan abubuwanmu da ƙarfi sosai don ɓoye ƙarin abubuwa daga ƙwarewar Asusun Matasa. Za mu kuma ƙara iyakance sakamakon Bincike, kuma mu kashe damar matasa ta gani, barin ko karɓar jawabai a ƙarƙashin aike.
Ƙarin Abubuwa: Matasa za su iya canjawa zuwa saitin 'Ƙarin Abubuwa' ne kawai da izinin iyaye, wanda iyaye za su iya samarwa ne kawai ta hanyar sa ido na iyaye. A wannan saitin, matasa za su ci gaba da amfana daga kariyar kai tsaye da ke ɓoye ƙarin abubuwa daga matasa fiye da yadda muke yi wa manya, kuma za mu ci gaba da cire abubuwa gaba ɗaya idan sun karya Tsarin Rayuwar Al'ummarmu. Koyaya, za a iya ba wa matasa shawarar wasu abubuwan da ba za su kasance a cikin saitunan 13+ da na Iyakantattun Abubuwa ba, kuma ba za mu ɓoye dukkan asusun da ke raba abubuwan da ba su dace da shekaru ba. Saitin Ƙarin Abubuwa ba zai samar da tsauraran taƙaicewar abubuwa ba a faɗin Kai tsaye, Jawabai, da Bincike ba waɗanda suke wani ɓangare na saitunan 13+ da na Iyakantattun Abubuwa.
Sanarwa: Akwai bambance-bambance da yawa tsakanin kafofin sada zumunta da fina-finai. Ba mu yi aiki da MPA ba lokacin da muke sabunta saitunan ƙunshiyarmu, kuma ba sa kimanta wani abu a Instagram da Facebook, kuma ba sa goyon baya ko amincewa da saitunan ƙunshiyarmu ta kowace hanya. Maimakon haka, mun yi koyi ne daga jagororin jama'a na MPA, waɗanda iyaye suka riga suka saba da su, da kuma martani daga iyaye. Tsarinmu na kula da ƙunshiya ba ɗaya yake da na hukumar sanya kimar fina-finai ba, don haka yanayin ƙwarewar na iya zama ba iri ɗaya bane gaba ɗaya.
Yadda Ake Bayar da Rahoton Abun Ciki Wanda Ya Saɓa Wa Dokoki
Muna aiki tuƙuru don gano abubuwan da suka karya dokokin mu, kuma muna samun yawancin abubuwan da muke cirewa ta hanyar amfani da fasahar mu kafin a kai mana rahoto. Idan ka ga wani abu da muka rasa, da fatan za a taimaka wajen sanya dandamalinmu ya zama wuri mai aminci ta hanyar bayar da rahoto a Facebook ko Instagram. Ana sakaya sunan duk rahotanni
Ƙarin Kayayyaki
Tsarin Rayuwar Al'ummar mu ya ƙunshi cikakkun bayanai kan nau'ikan abubuwan da muke cirewa da kuma ƙayyadewar shekaru ga kowane yanki na doka. Dominn karanta su, danna nan.
Mun kuma ƙirƙiro fasaha da ke aiki tuƙuru wurin gano manya da suke abun zargi, kamar babba wanda matasa suka toshe ko suka bayar da rahotonsa akai-akai, ko kuma idan babba yana neman abun ciki da ya saɓa wa dokoki akai-akai. Ba za mu ba da shawarar manya da suke abun zargi ba ga matasa, kuma ba za mu ba da shawarar matasa ga manya abun zargi ba. Kana iya ƙara karatawa game da wannan a nan.
Za ka iya ƙara karantawa game da hanyoyin da muke taimaka wa don kiyaye tsaro al'ummar mu a Cibiyar Tsaro, da kuma hanyoyin da muke tallafa wa matasa da iyalai a Cibiyar Iyali.